Connect with us

News

Gwamnatin Legas Ta Kama Mabarata 62 A Kan Tituna 

Published

on

53 1 (1)

Jami’an Hukumar Kula da Tsabtace Muhalli ta Jihar Legas (KAI) sun kama mutane 62, ciki har da mutum 29 da ake zargi da yin bara da kuma yara 33 da ake zargin ana amfani da su wajen yin bara a tituna.

An kama mutanen ne yayin wani samame da jami’an hukumar suka gudanar a yankunan Ajah da Lekki da ke jihar.

Lagos, Kano, Kaduna Na Kan Gaba Wajen Yawan Masu Rajistar Zaɓe – INEC

Kwamishinan Gidaje da Tsare-tsaren Birane na Jihar Legas, Tokunbo Wahab, ne ya bayyana hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Lahadi.

Ya ce samamen ya mayar da hankali ne kan mutanen da ke yin bara a tituna, musamman yaran da ake zargin ana amfani da su wajen yin bara ba bisa ƙa’ida ba.

Kwamishinan ya ce, “Jami’an Hukumar Kula da Tsabtace Muhalli ta Jihar Legas sun kama mutane 62, waɗanda suka haɗa da ’yan bara 29 da yara 33 da ake zargin ana amfani da su wajen yin bara ba bisa ƙa’ida ba, yayin wani samame da aka gudanar a yankunan Ajah da Lekki na Jihar Legas.”

Advertisement

Ya ƙara da cewa matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na tabbatar da tsaftar muhalli da kuma dakile amfani da yara wajen bara a tituna.

 

PUNCH

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending