Connect with us

News

Gobara Ta Tashi A Kasuwar Singa Da Ke Kano

Published

on

Spread the love

Rahotanni na gaggawa sun tabbatar da cewa an samu tashin gobara a kasuwar Singa da ke Bello Road, cikin birnin Kano, lamarin da ya tayar da hankulan ’yan kasuwa da mazauna yankin.

Bayanan da Jaridar INDA RANKA ke samu sun nuna cewa gobarar ta tashi ne a safiyar yau, inda wutar ta fara cin wasu sassan kasuwar, lamarin da ya haddasa asarar kayayyaki da dukiyoyin ’yan kasuwa.

Gobara Ta Tashi A Kasuwar Singa Da Ke Kano

Advertisement

Wasu daga cikin mutanen da suka fara kai dauki a wajen sun shaida  cewa ana matukar bukatar ɗaukin gaggawa, musamman daga jami’an kashe gobara, domin dakile yaduwar wutar da rage barnar da ake fuskanta.

Ya zuwa lokacin kammala wannan rahoto, ba a tabbatar da musabbabin gobarar ko asarar rayuka ba, yayin da jami’an tsaro da na agaji ke ci gaba da kokarin shawo kan lamarin.

 

Advertisement
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *