News
Gwamnan Kano Ya Yi Sabbin Naɗe-Naɗe
Gwamnan Jihar Kano ya naɗa Abubakar Ibrahim Matawalle a mai riƙon Babban Daraktan Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar.
Wannan na cikin sanarwar da Daraktan Yada Labaran Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Litinin 2 ga Fabrairu 2026.
Jami’an ‘Yan Sanda Sun Kwato Alburusai 415 , Sun Kama Direba Da Fasinjoji A Akwa Ibom
Sanarwar ta bayyana cewa Abubakar Ibrahim Matawalle ya taba rike mukamin Babban Sakataren Hukumar Jin Daɗin Alhazan a baya, tare da rike mukamin babban sakatare a ma’aikatar kula da ma’aikata kafin ritayarsa daga aikin gwamnati.
Matawalle ya yi ritaya daga aikin gwamnati a shekarar 2014 bayan shafe shekaru a matsayin babban sakatare, kuma ya taba jagorantar harkokin aikin hajji a lokuta daban-daban a jihar Kano.
Sanarwar ta ce, naɗin nasa na daga cikin matakan da gwamnatin jihar ke dauka na cike guraben mukamai domin inganta tafiyar da muhimman hukumomin gwamnati, inda sanarwar ta ce nadin ya fara aiki nan take.
