News
Dakarun Soji Sun Cafke Wanda Ake Zargi Da Ta’addanci, Sun Ƙwato Makamai A Kano
Dakarun Rundunar Sojin Nijeriya ta Birged ta 3 sun kama wani mutum da ake zargi da hannu a ayyukan ta’addanci tare da ƙwato makamai da wasu kayayyaki masu alaƙa da aikata laifuka a wani samame da suka kai a Ƙaramar Hukumar Ɗambatta da ke Jihar Kano.
Majiyoyin tsaro sun shaida wa PRNIGERIA cewa an gudanar da samamen ne da misalin ƙarfe 10:30 na dare a ranar 21 ga Yuni, 2026, bayan samun sahihan bayanan sirri kan wata maɓoyar da ake zargin ɓata-gari na amfani da ita a ƙauyen Kwanan Dumawa.
Jamhuriyar Nijar Ta Miƙa Buƙatar Ficewa Daga Kotun Hukunta Manyan Laifuka Ta Duniya ICC
Rahotanni sun nuna cewa dakarun sun kai farmakin cikin tsanaki, inda suka yi nasarar cafke wanda ake zargin tare da ƙwato wasu kayayyaki da ake kyautata zaton suna da alaƙa da ayyukan ta’addanci da sauran laifuka.
Kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da bindigar toka guda ɗaya, ƙaramar bindigar gargajiya, bindigar ƙirar pistol, mazubin alburusai huɗu, wuƙaƙe uku, wayoyin hannu biyu, almakashi biyu, katin shaida, guru da kuma katin cirar kuɗi na ATM.
Majiyoyin sun ce wanda aka kama na ci gaba da tsare a hannun jami’an tsaro domin zurfafa bincike kan zarge-zargen da ake masa da kuma gano yiwuwar alaƙarsa da wasu masu aikata laifuka.
Hukumomin soji sun bayyana cewa samamen na daga cikin matakan da suke ɗauka domin daƙile ayyukan miyagu da hana bazuwar masu aikata ta’addanci a Kano da sauran yankunan da ke maƙwabtaka da jihar.
Sun kuma jaddada aniyarsu ta ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro bisa bayanan sirri domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma da tabbatar da zaman lafiya a faɗin ƙasar nan.
-
News6 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News3 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News6 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
