Connect with us

News

Dakarun Soji Sun Gano Wajen Haɗa Makamai A Cross River

Published

on

1773443692288

Rundunar Sojojin Najeriya ta sanar da gano wani wajen ƙera makamai ba bisa ƙa’ida ba tare da hallaka wasu ‘yan bindiga biyar a ƙaramar hukumar Obubra da ke jihar Cross River.

‎A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ta 13 Brigade, Manjo Yemi Sokoya, ya fitar ranar Juma’a, ya ce dakarun rundunar sun samu wannan nasara ne yayin wani samame da suka kai a ƙauyen Odonget da ke yankin.

Advertisement

‎Gwamnatin Tarayya Ta Yi Gargaɗin Za A Iya Samun Ɓullar Cutar Sanƙarau A Kano Da Wasu Jihohi 10 ‎

‎Sanarwar ta ce rundunar da ke ƙarƙashin kulawar Hedikwatar Sojoji ta 82 Division ta ƙaddamar da farmakin ne bayan wani hari da wasu masu ɗauke da makamai suka kai wa jami’an tsaro, waɗanda suka amsa kiran gaggawa sakamakon rikicin al’umma a yankin.

Advertisement

‎A cewar rundunar, tsakanin ranakun 12 zuwa 13 ga watan Maris, sojojin sun gudanar da sintiri da bincike a wuraren da ake zargin maharan na ɓuya domin gano su.

‎A ranar 13 ga Maris ne dakarun suka sake cin karo da ‘yan bindigar, inda aka yi musayar wuta, lamarin da ya yi sanadin hallaka biyar daga cikinsu, yayin da wasu suka tsere.

Advertisement

‎Bayan samamen, sojojin sun gano wani wuri da ake zargin ana ƙera makamai a ɓoye, wanda ake kyautata zaton ana amfani da shi wajen samar da makaman da ake amfani da su wajen aikata hare-hare a yankin.

A binciken da aka yi a wurin, sojojin sun kwato mujallun bindigar AK-47 guda uku, da bindigogi 10 da aka ƙera a gida, tare da wasu kayan aikin da ake amfani da su wajen haɗa makamai.

Advertisement

‎Daga bisani rundunar ta lalata wajen ƙera makaman domin hana ci gaba da amfani da shi wajen aikata laifuka.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending