Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Ƙera Makamai Da Harsasai A Cikin Ƙasa

Published

on

184b9bf3509eb84b17dffd5742363975893bf930e3cb6d441ebd84ecf4c9b821

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatin tarayya za ta hanzarta samar da masana’antu a cikin ƙasa domin ƙera makamai da harsasai, da nufin ƙarfafa tsarin tsaron ƙasa tare da rage dogaro da ƙasashen waje.

Tinubu ya bayyana haka ne a ranar Juma’a a Abuja, yayin bikin kammala karatun Course 33 na Kwalejin Tsaro ta Ƙasa (NDC), inda Mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima, ya wakilce shi.

Advertisement

Dalibai Na Yin Karatu A Kasan Bishiyu Saboda Rushewar Aji A Kano 

Shugaban Ƙasar ya ce samar da kayan aikin tsaro a cikin gida zai taimaka wajen fuskantar matsalolin tsaro da ƙarfin gwiwa, tare da ba da damar dogaro da kai a fannin tsaro.

“Ƙarfafa masana’antun cikin gida zai rage dogaro da ƙasashen waje, kuma zai taimaka wajen magance barazanar tsaro a ƙasar nan,” in ji Tinubu.

Advertisement

Tinubu ya yaba da taken horon Course 33 na Kwalejin Tsaro mai taken “Ƙarfafa Hukumomi Don Tsaro da Ci Gaban Ƙasa”, inda ya ce ƙasashen da suka ci gaba sun yi hakan ne ta hanyar samun hukumomi masu ƙarfi da juriya.

“Hukumomi masu ƙarfi su ne ke tabbatar da doka, kare haƙƙin ’yan ƙasa, samar da shugabanci nagari da kuma tsare-tsare masu amfani. Wannan shi ne dalilin da ya sa gwamnati ta sanya ƙarfafa hukumomi a matsayin babban buri na ƙasa,” in ji shi.

Advertisement

Ya ce gwamnati za ta ci gaba da ba da muhimmanci wajen samar da kayan aiki na zamani ga jami’an tsaro domin inganta tsaro a fadin ƙasar.

Daliban Course 33 na Kwalejin Tsaro ta Ƙasa sun haɗa jami’an soji na ƙasa, ruwa, sama, da kuma jami’an tsaro daga wasu ƙasashen waje.

Advertisement

Shugaban Ƙasar ya bayyana cewa ilimin da aka koya wa daliban zai taimaka wajen ƙarfafa hukumomin tsaro da inganta zaman lafiya a Najeriya da ƙasashen da suka fito.

 

Advertisement

TRT GLOBAL 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending