Connect with us

News

Sarkin Musulmi Ya Sanar Da Litinin A Matsayin 1 Ga Watan Rabi’ul Awwal

Published

on

Sarkin Musulmi kuma shugaban Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci (NSCIA), Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya sanar da Litinin a matsayin ranar farko ta watan Rabi’ul Awwal, 1447 bayan hijira.

Wannan sanarwar ta fito ne daga bakin Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Junaidu, wanda kuma shi ne shugaban majalisar shawarwari ta fadar Sarkin Musulmi, a daren Asabar.

Advertisement

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Ƙera Makamai Da Harsasai A Cikin Ƙasa

A cewar Farfesa Junaidu, hukumar duban wata ta kasa ta tabbatar da cewa ba a samu ganin jaririn watan Rabi’ul Awwal ba a daren Asabar a ko’ina cikin Najeriya, lamarin da ya sanya aka ƙayyade Litinin a matsayin farkon watan.

Haka zalika ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su ci gaba da gudanar da ibadoji da yin addu’o’in alheri ga ƙasa da al’ummar musulmin a wannan wata mai albarka.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending