News
Dalibai Na Yin Karatu A Kasan Bishiyu Saboda Rushewar Aji A Kano
Daliban makarantar firamare a unguwar Turawa, karamar hukumar Karaye, Jihar Kano, na gudanar da karatunsu a fili ƙarƙashin bishiyu, bayan rushewar mafi yawan gine-ginen makarantar.
Rahoton jaridar Solacebase ya nuna cewa daga cikin dakunan karatu guda shida da makarantar ke da su, uku sun rushe gaba ɗaya, biyu kuma sun rasa rufi, yayin da ɗakin da ke aiki shi kaɗai bai da bene. Wannan matsala ta tilasta ɗaliban zama a ƙasa domin karatu.
Dakarun Sojin Sama Sun Kashe ’Yan Ta’adda 35 A Iyakar Nijeriya Da Kamaru
Malaman makarantar sun ce duk lokacin da aka samu ruwan sama, sai sun rufe makaranta domin kare lafiyar yara, abin da ke kawo tsaiko a jadawalin koyarwa.
Iyayen yara a yankin sun nuna damuwa matuƙa kan halin da makarantar ke ciki, suna roƙon gwamnatin jihar da ta ɗauki mataki cikin gaggawa.
“Yaranmu ba za su iya yin gogayya da sauran yara a birane ba idan har za su ci gaba da karatu a ƙarƙashin bishiyu,” in ji Malam Haruna Ibrahim, ɗaya daga cikin iyaye a yankin.
Shugaban Kungiyar Iyaye da Malamai (PTA), Malam Sulaiman Idris, ya ce sun sha rubuta koke-koke zuwa hukumomi, amma babu wani mataki da aka ɗauka.
Shugaban al’ummar yankin, Nazifi Ibrahim Muhammad, ya yi kira ga gwamnati da kungiyoyin tallafi da su taimaka wajen sake gina makarantar.
Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Alhaji Ali Bukar Makoda, ya ce gwamnatin jihar ta gaji makarantu da dama a lalace, kuma tana ci gaba da gyare-gyare a matakai daban-daban.
