Connect with us

News

‎Dakarun Sojin Sama Sun Kashe ’Yan Ta’adda 35 A Iyakar Nijeriya Da Kamaru

Published

on

Wani Jirgin Rundunar Sojin Saman Najeriya Ya Hallaka Mutane Da Dama A Sokoto 

Dakarun Sojin Saman Nijeriya (NAF) sun kashe aƙalla ’yan ta’adda 35 a harin sama da suka kai iyakar Nijeriya da Kamaru.

‎Mai magana da yawun NAF, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya ce sun kai harin ne da sassafe a ranar Asabar, 23 ga watan Agusta, 2025, ƙarƙashin Operation Hadin Kai (OPHK).

Advertisement

Jami’an NDLEA Sun Kama Matashi Dauke Da Taba Wiwi Mai Darajar Sama Da Naira Miliyan 10 A Kano

‎Ya bayyana cewa ’yan ta’addan sun taru a kusa da iyakar bayan sun yi ƙoƙarin kai wa sojojin ƙasa hari a yankin Kumshe.

‎Bayan samun bayanan sirri, NAF ta kai hare-hare a wurare huɗu da aka gano, inda ta kashe sama da ‘yan ta’adda 35.

Advertisement

‎Bayan kammala aikin, sojojin ƙasa sun tabbatar da cewa an kwantar da tarzomar a yankin.

‎Ejodame ya ƙara da cewa rundunar sojin sama za ta ci gaba da tallafa wa sojojin ƙasa tare da tarwatsa ’yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas.

Advertisement

‎Shugaban sojin sama na ƙasa, Air Marshal Hasan Bala Abubakar, ya yaba da ƙwarewar dakarun tare da tabbatar da cewa za su ci gaba da kai hare-hare bisa bayanan sirri domin murkushe ’yan ta’addan da ke barazana ga tsaron Nijeriya.

 

Advertisement

 

LEADSHIP

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending