Connect with us

News

Muhimman Abubuwan Da Suka Faru A 2025 A  Najeriya ‎

Published

on

FB IMG 1767267129466
Spread the love

Yayin da muke bankwana da shekarar 2025, mun tattara muku wasu daga cikin muhimman abubuwa da suka a Najeriya,a fannoni da dama da suka haɗa da tattalin arziƙi da tsaro da siyasa da dai sauransu.

‎Fitattun mutanen da suka rasu a 2025

‎Bara mu fara da tunawa da manyan rashe-rashen da Najeriya ta yi a 2025, na tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari, da attajirin ɗan kasuwar nan, Alhaji Aminu Dantata, da shehin malamin nan, Dr Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi, da jagoran ɗarikar Tijjaniya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, mutuwar waɗannan fitattun mutane ta gigita ƴan ƙasar sosai.

‎    Ɓangaren Tsaro

Advertisement

‎A shekara ta 2025 ne aka fara yaɗa jita-jitar juyin mulki a Najeriya, bayan nan shugaba Tinubu ya kori dukkan manyan hafsoshin tsaron ƙasar tare da maye gurbinsu da wasu.

‎Bayan murabus ɗin ministan tsaron Najeriya, Badaru Abubakar ne kuma a cikin shekarar, Tinubu ya naɗa janar Christopher Musa a matsayin wanda zai gaje shi.

‎A watan Oktoba ne shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin soji akan Najeriya, saboda zargin da yake cewa ana kisan kiristoci a ƙasar, zargin da gwamnatin ƙasar ta musanta.

‎Daga nan ne kuma aka fara ganin tsanantar hare-haren ƴan bindiga a ƙasar musamman a yankin arewaci.

Advertisement

‎Inda ƴan bindiga suka sace ɗalibai mata 25 daga makarantar sakandiren Maga dake jihar Kebbi, sai harin da aka kai mujami’ar jihar Kwara inda aka sace masu ibada fiye da 30, kana ƴan bindiga sun sace wasu ɗalibai 300 a jihar Neja daga makarantar St Mary’s dake Papiri.

‎Daga bisani gwamnati ta sanar da ƙubutar da dukkan waɗannan ɗalibai da masu ibada da aka sace, tare da miƙa su hannun iyalansu.

‎Ana gab da ƙarƙare shekara ta 2025 ɗin ne kuma a ranar  26 ga watan Disamba aka tashi da labarin da ya gigita ƴan Najeriya, wato harin da Amurka ta kai a jihar Sokoto, wanda ta kira kan ƴan ta’addan IS dake addabar ƙasar, kodayake gwamnatin Najeriya ta ce ita ta bai wa Washington bayanan sirri kan yadda za ta ƙaddamar da shi.

‎A dai cikin shekarar ne kuma kotu ta yanke wa  jagoran ƴan awaren BIAFRA Nnamdi Kanu hukuncin ɗaurin rai da rai a gidan yari, bayan tabbatar da zargin ta’addanci da ake masa.

Advertisement

‎Ɓangaren siyasa

‎A watan Fabrairu ne rikici ya ɓarke a majalisar datttawan Najeriya, tsakanin ƴar majalisar Kogi Sanata Natasha Akpoti, da shugaban majalisar Godswill Akpabio da ta zarge shi da yunƙurin cin zarafinta, lamarin da ya kai ga dakatar da ita na tsawon watanni 6.

‎A watan Maris, shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanya dokar ta ɓaci a jihar Ribas, inda ya dakatar da gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa da dukkan ƴan majalisar dokokin jihar, tare da naɗa kwantoman da zai jagorance ta har na tsawon watanni shida.

Advertisement

‎Daga bisani dai an janye wannan doka a watan Satumba.

‎A watan Yuli ne kuma jiga-jigan ƴan adawa a Najeriya da suka haɗa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da ɗan takarar shugaban ƙasa a zaben 2023 Peter Obi suka zaɓi haɗewa a jam’iyyar ADC domin tunkarar jam’iyyar APC mai mulki a zaɓen 2027.

‎A wani abu mai kama da shirye-shiryen zaɓen na 2027, ƴan adawa suka fara sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki, ciki har da gwamnoni 6 da tarin ƴan majalisun tarayya.

‎A watan Nuwamba ne kuma shugaba Tinubu ya naɗa Farfesa Joash Amupitan a matsayin sabon shugaban hukumar zaɓen ƙasar INEC, bayan ƙarewar wa’adin Farfesa Mahmud Yakubu, kuma a watan ne sabon shugaban ya tunkari zaɓen gwamnan jihar Anambra, wanda Charles Soludo na APGA ya sake lashewa.

Advertisement

‎A cikin shekara ta 2025 ɗin ne kuma, bayan bai wa ƙananan hukumomi ƴancin cin gashin kansu, shugaba Tinubu ya yi barazanar fara aike musu da kuɗaɗensu kai tsaye daga asusun tarayya, saboda yadda gwamnonin jihohin ƙasar suka ƙi fara aiwatar da umarnin kotun ƙolin.

‎Batun afuwar  da shugaba Tinubu ya yiwa wasu fitattun mutane a ƙasar ya bar baya da ƙura, musamman Maryam Sanda da ta kashe mijinta, bayan shan matsin lamba ne Tinubu ya janye sunanta daga cikin waɗanda ya yiwa afuwar.

 

‎Bari muje ga fannin tattalin arziƙi

Advertisement

‎A watan Yuni, shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu kan sabbin dokokin haraji guda 4, waɗanda ke ci gaba da janyo zazzafar muhawara, kuma ake shirin fara amfani dasu a ranar 1 ga watan Janairun 2026.

‎Rikicin matatar Dangote da masu ruwa da tsaki a harkar mai na ƙungiyoyin PENGASSAN da NUPENG ya durƙusar da harkokin mai a Najeriya, rikicin ya soma ne bayan da Aliko Dangote ya sanar da shirinsa na fara rarraba man fetur zuwa sassan ƙasar.

‎Sai rikicin da ya kunno kai tsakanin Dangote da shugaban hukumar NMDPRA, Farouk Ahmed, inda attajirin Afrikan ya zarge shi da da zagon ƙasa da facaka da dukiyar ƴan Najeriya, lamarin da ya kai ga murabus ɗin Farouk.

 

Advertisement

 

RFI

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *