Labarai
Amurka Ta Kakaba Takunkumi A Kan Wani Dan Canji Dan Najeriya Da Kamfanoni Uku A Kano Da Largos

kan wani dan canji
Gwamnatin Amurka ta sanya wani ɗan Najeriya da kamfanoni uku masu gudanar da harkokin canjin kuɗi a jihohin Kano da Legas cikin jerin waɗanda ta kakaba wa takunkumi, bisa zargin taimakawa wajen safarar kuɗaɗen da ke da alaƙa da ƙungiyar ta’addanci ta ISIS.
A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fitar, ta bayyana cewa mutumin da abin ya shafa, Mukhtar Adamu Muhammad, na daga cikin mutane uku da kamfanoni shida da aka ɗora wa takunkumin saboda zargin taka rawa wajen samar da hanyoyin tafiyar da kuɗaɗe domin ayyukan ISIS a sassa daban-daban na duniya.
Cutar Kwalara Ta Hallaka Mutane 108, Sama Da 13,000 Sun Kamu A Borno
Sanarwar ta ce Mukhtar Adamu Muhammad na da alaƙa da ƙungiyar ISIS ta Yammacin Afirka (ISWAP), wadda ke gudanar da hare-hare a yankin Tafkin Chadi da wasu sassan Arewacin Najeriya.
Kamfanonin da aka ambata cikin takunkumin sun haɗa da Generation Currency Bureau de Change Limited da Manhattan Bureau de Change Limited, dukkansu da ke Kano, sai kuma Nine to Nine Exchange Bureau de Change Limited da ke Legas.
Gwamnatin Amurka ta bayyana cewa matakin wani ɓangare ne na ƙoƙarin da take yi na dakile hanyoyin samun kuɗaɗen ƙungiyoyin ta’addanci, tare da hana su ci gaba da gudanar da ayyukansu a faɗin duniya.
Ta kuma jaddada cewa za ta ci gaba da haɗa kai da ƙasashen duniya domin gano da kuma toshe hanyoyin da ƙungiyoyin ta’addanci ke amfani da su wajen tara da safarar kuɗaɗe domin aiwatar da hare-harensu.
Takunkumin na nufin toshe duk wasu kadarori ko mu’amalolin da waɗanda aka sanya wa takunkumin ke da su a ƙarƙashin ikon Amurka, tare da hana ‘yan ƙasa da kamfanonin Amurka gudanar da duk wata hulɗar kasuwanci da su..
-
Labarai7 days ago
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Yi Wa Masu Digirin Ƙasashen Waje Jarrabawa
-
Labarai3 days ago
Jami’an Tsaro A Pakistan Sun Kama ’Yan Najeriya 20 Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi
-
Labarai2 days ago
Hare-haren Ta’addanci Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 835 A Najeriya Cikin Wata Guda – Rahoto
