News
Majalisar Dattawa Ta Amince Da Kudirin Samar Da ‘Yansandan Jihohi
Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da ƙudirin gyaran kundin tsarin mulki da ke neman kafa rundunar ‘yan sandan jihohi a faɗin ƙasar, a wani mataki da ake kallon zai kawo sauyi a tsarin tsaron Najeriya.
Amincewar ta zo ne a zaman majalisar na ranar Laraba, bayan da sanatoci suka yi muhawara tare da nazari kan ƙudirin kafin su amince da shi.
Amurka Ta Kakaba Takunkumi A Kan Wani Dan Canji Dan Najeriya Da Kamfanoni Uku A Kano Da Largos
Ƙudirin na da nufin bai wa jihohi damar kafa rundunonin ‘yan sanda nasu domin taimakawa wajen inganta tsaro, yaƙi da laifuffuka, da kuma magance matsalolin tsaro da suka shafi yankunansu.
Masu goyon bayan ƙudirin sun bayyana cewa kafa ‘yan sandan jihohi zai taimaka wajen kusantar jami’an tsaro da al’umma, tare da ba da damar ɗaukar matakan gaggawa kan matsalolin tsaro a matakin jiha.
Sai dai wasu masu ruwa da tsaki sun nuna damuwa kan yiwuwar amfani da rundunar wajen cimma muradun siyasa, lamarin da ya sa ake kira da a samar da ingantattun matakan sa ido da kariya domin hana cin zarafi.
Amincewar Majalisar Dattawa na zuwa ne bayan shafe shekaru ana muhawara kan bukatar sake fasalin tsarin tsaron Najeriya, musamman duba da ƙalubalen rashin tsaro da ke addabar sassa daban-daban na ƙasar.
Ana sa ran ƙudirin zai bi sauran matakan da kundin tsarin mulki ya tanada kafin ya zama doka.
