Connect with us

News

Farfesa Gwarzo @ 48: PRNigeria da Kamfanin Adnan Mukhtar Sun Horar da ’Yan Jarida Kan Amfani Da Fasahar AI

Published

on

Public Lecture held at PR Nigeria office Kano 1200x904
Spread the love

Ofishin PRNigeria ya shirya wata laccar jama’a tare da taron karramawa a ranar Alhamis, domin murnar cikar Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, wanda ya kafa Rukunin Jami’o’in Maryam Abacha American University of Nigeria (MAAUN), shekaru 48 a duniya.

Taron, wanda aka gudanar a ofishin PRNigeria da ke Kano, ya haɗa ’yan jarida, masana ilimi da ƙwararru a fannin hulɗa da jama’a, inda aka mayar da hankali kan rawar da Fasahar Ƙirƙirarriyar Basira (Artificial Intelligence – AI) ke takawa a aikin jarida na zamani, tare da tattauna ƙalubalen ɗabi’a da sahihancin labarai.

Dubu 100 Aka Biya Ni Na Sanya Bam A Masallaci Da Ke Maiduguri — Ɗan Ƙunar Baƙin 

An gabatar da laccar ne ƙarƙashin taken “AI and the Emerging Trends of Online Newspapers: Reflections on the Ethics of Journalism,” inda masu jawabi suka jaddada muhimmancin kare ƙa’idojin aikin jarida a wannan zamani da kafafen yaɗa labarai ke ƙara dogaro da fasahar zamani.

Shugaban Rukunin Jami’o’in MAAUN, Farfesa Mohammad Israr, ya bayyana cewa jami’ar ta zama ta farko a Arewacin Najeriya da ta samu cikakken zama mamba a Ƙungiyar Masana Hulɗa da Jama’a ta Najeriya (NIPR).

Advertisement

A cewarsa, wannan nasara na nuna ƙudurinsu na inganta sadarwa mai ɗabi’a, tare da samar da ilimi da ya dace da buƙatun zamani.

Farfesa Israr ya ƙara da cewa sashen Mass Communication na MAAUN zai ci gaba da fitar da ƙwararrun ɗalibai da za su taka muhimmiyar rawa a harkar kafafen yaɗa labarai, musamman a Kano da ma faɗin Najeriya.

Da yake jawabi, Editan PRNigeria, Yusha’u Shuaibu, ya ce an shirya taron ne domin karrama gudummawar da Farfesa Gwarzo ke bayarwa wajen bunƙasa ilimi da aikin jarida, musamman a Arewacin ƙasar.

“Mun ga dacewar karrama mutum da ya sadaukar da rayuwarsa wajen ci gaban ilimi da gina ɗan Adam,” in ji Shuaibu.

Advertisement

A wajen laccar, Manajan Ayyukan PRNigeria, Muhammad Dahiru Lawan, ya yi gargadin cewa duk da sauƙin da AI ke kawowa a jaridun intanet, ’yan jarida su guji sakaci wajen duba sahihanci da ɗabi’ar labarai.

Shi ma Shugaban Gidauniyar Adamu Abubakar Gwarzo, Dakta Musa Sufi, ya ja hankalin mahalarta kan illolin dogaro kacokan da AI, yana mai cewa fasaha ba za ta taɓa maye gurbin basirar ɗan jarida ba.

“AI kayan taimako ne, ba madadin ƙwarewa ba,” in ji shi.

A nasa bangaren, Adnan Mukhtar, shugaban kamfanin hulɗa da jama’a na Adnan Mukhtar and Associates, ya bayyana Farfesa Gwarzo a matsayin jagoran ilimi da ya sadaukar da rayuwarsa wajen gina ƙwararru.

Advertisement

Ya ce kafa MAAUN ya kasance sakamakon jajircewa da hangen nesa na Farfesa Gwarzo wajen bunƙasa jarin ɗan Adam a Najeriya.

Taron ya ƙare da taya Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo murnar cikar sa shekaru 48, tare da yi masa fatan tsawon rai da ci gaba da hidima ga al’umma.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *