News
Jami’an NDLEA Sun Kama Matashi Dauke Da Taba Wiwi Mai Darajar Sama Da Naira Miliyan 10 A Kano
Jami’an Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), reshen Kano, sun cafke wani matashi mai shekaru 27, Umar Adamu-Umar, dauke da kilogiram 9 na tabar wiwi, wacce aka kiyasta darajarta fiye da Naira miliyan goma.
Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar a Kano, Sadiq Muhammad-Maigatari, ya fitar a ranar Asabar, 23 ga watan Agusta, ta tabbatar da kama matashin a ranar 6 ga watan Agusta, a kan hanyar Zariya zuwa Kano, ta hannun jami’an NDLEA na ofishin hukumar na karamar hukumar Kiru.
A cewar sanarwar, Umar na jigilar kunshi 19 na tabar wiwi daga jihar Legas zuwa Kano lokacin da aka cafke shi. “Wanda ake zargin ya amsa laifinsa, ya kuma bayyana cewa ya dade yana harkar fataucin miyagun kwayoyi, kuma hukumar ta dade tana sa ido a kansa,” in ji Maigatari.
Jami’in ya ce wannan samame ya yi wa hanyar safarar miyagun kwayoyi cikas, ya kuma rage kudaden da masu harkar ke samu don ci gaba da aikata laifuka.
“Cire irin wannan yawan miyagun kwayoyi daga hannun mutane na taimakawa wajen kare al’umma, musamman matasa da ke cikin hadarin fadawa wannan mummunar dabi’a,” in ji shi.
Maigatari ya kara da cewa hukumar NDLEA a Kano karkashin jagorancin Abubakar Idris-Ahmad za ta ci gaba da kai farmaki tare da amfani da bayanan sirri don dakile fataucin miyagun kwayoyi a jihar.
