Connect with us

News

Dakarun Soji Sun Kashe ’Yan Bindiga 9 Bayan Sun Yi Artabu Da Su A Kano 

Published

on

‎Burkina Faso ta saki sojojin Najeriya Da Take Rike Da Su Na Tsawon Kwanaki 10
Spread the love

Dakarun Sojin Najeriya sun kashe ’yan bindiga tara bayan sun yi artabu da su a Ƙaramar Hukumar Shanono ta Jihar Kano.

Lamarin ya faru ne a daren ranar Asabar a garuruwan Bakaji da Unguwar Garma, da ke yankin Goron Dutse, bayan ’yan bindiga sun kai hari yankin.

Dakarun Soji Sun Kashe ’Yan Ta’adda 438 Na Boko Haram da ISWAP Cikin Watanni Bakwai

Shugaban Kwamitin Tsaron Al’umma na Shanono/Bagwai, Alhaji Yahya Bagobiri ne, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi kamar yanda Jaridar AMINIYA ta ruwaito

Ya ce ’yan bindigar sun shiga yankin ne a daren ranar Asabar, inda suka yi musayar wuta da sojoji na tsawon sa’o’i.

Advertisement

A cewarsa, wani ɗan sa-kai ya rasa ransa yayin artabun, yayin da wani kuma ya ji rauni.

Bagobiri, ya ce ’yan bindigar sun ja da baya ne bayan sojoji sun yi musu ruwan wuta, amma daga bisani suka dawo da yawa da safiyar ranar Lahadi.

“Sojoji sun kashe wasu daga cikin ’yan bindigar tare da ƙwato babura. Amma da misalin ƙarfe 5 zuwa 6 na safe, ’yan bindigar sun sake dawowa suka buɗe wa sojoji wuta, amma duk da haka ba su samu damar shiga yankin ba,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa duk da ƙoƙarin da sojojin suka yi, ’yan bindigar sun yi garkuwa da mutane shida tare da sace shanu kusan 40.

Advertisement

“Saboda sun zo da yawa sosai, sun yi garkuwa da mutane shida kuma sun kwashe shanu 40.

“Amma muna godiya ga sojoji da suka mayar da martani tare da suka kashe ’yan bindiga tara, lamarin da ya sa suka bar babura da dama,” in ji Bagobiri.

Ya kuma bayyana cewa daga baya ’yan bindigar sun sake komawa yankin domin ɗaukar gawarwakin waɗanda aka kashe.

“Ina matuƙar yaba wa sojoji bisa yadda suka kare yankin tare da hana ’yan bindiga yin ɓarna.

Advertisement

“Sun cancanci yabo domin a wancan lokaci babu wanda zai iya fitowa daga gidansa,” in ji shi.

Da aka tuntuɓi Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojin Ƙasa ta Brigade ta 3, Kyaftin Babatunde Zubairu, ya tabbatar da faruwar artabun.

Sai dai ya ce ba zai iya tabbatar da adadin ’yan bindigar da aka kashe ba.

“E, an yi artabu, kuma wani ɗan sa-kai ya ji rauni. Mun ƙwato babura uku da wayoyin salula biyu masu ɗauke da jinin mutane,” in ji Zubairu.

Advertisement

Idan ba a manta ba, a watan Oktoba, dakarun Rundunar Haɗin Gwiwa ta Operation MESA, sun kashe aƙalla ’yan bindiga 19 a Ƙaramar Hukumar Shanono a jihar.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *