Connect with us

News

Mutane Da Dama Sun Jikkata Yayin Da Mota Ta Murkushe Adaidaita Sahu ‎

Published

on

FB IMG 1779099154758

Mutane da dama sun samu raunuka sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya faru a safiyar Litinin a yankin Federal Bus Stop da ke kan titin Ipaja a jihar Legas.

‎Rahotanni sun bayyana cewa hatsarin ya auku ne da misalin karfe 8:50 na safe, inda wata mota kirar Honda ta murkushe masu adaidaita sahu gud biyu.‎

Advertisement

‎Shaidu sun ce matar da ke tukin motar na tafiya cikin matsanancin gudu ne lokacin da ta yi kokarin kauce wa wani ma’aikacin Hukumar Tsaftar Muhalli ta Jihar Legas (LAWMA) da ke share titi.

‎A cewar wadanda suka shaida lamarin, motar ta fara buge ma’aikacin kafin daga bisani ta haye daya bangaren titin tare da fadawa cikin adaidaita sahu biyun.

Advertisement

Jaridar Punch ta ruwaito cewa akalla fasinjoji 10 ne suka samu raunuka daban-daban a hatsarin.

An garzaya da wadanda suka jikkata zuwa wani asibiti mai zaman kansa domin ba su agajin gaggawa, kafin daga bisani aka mayar da wasu daga cikinsu zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Legas (LASUTH) da ke Ikeja domin ci gaba da kula da lafiyarsu.

Advertisement

‎Jami’an ’yan sanda daga ofishin Gowon Division, tare da jami’an sintirin unguwa da na Hukumar LASTMA, sun isa wurin domin shawo kan cunkoson ababen hawa tare da gudanar da aikin ceto.

‎Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomi ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan hatsarin ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending