Connect with us

News

Ruwan Sama Da Iska Lalata Gidaje Sama Da 100 A Burum Burum

Published

on

IMG 20250909 WA0037

Al’ummar Burum Burum da ke ƙaramar hukumar Tudunwada a Jihar Kano sun shiga cikin damuwa bayan ruwan sama mai ƙarfi da iska suka sauka a daren Litinin, lamarin da ya janyo rushewar gidaje fiye da 100 tare da lalata rufin wasu gidajen da dukiyoyi masu tarin yawa.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, duk da barnar da aka tafka, babu wanda ya rasa ransa, sai dai wasu daga cikin mazauna garin sun jikkata.

Advertisement

Sama Da Mutum Miliyan 3.5 Ne Suka Yi Rijistar Katin Zaɓe Ta Yanar Gizo – INEC

Babban limamin masallacin Juma’a na garin, Imam Auwal Imam, ya bayyana cewa lamarin ya girgiza al’umma, inda ya yi kira ga hukumomi da su kawo musu agajin gaggawa kafin halin da suke ciki ya ƙara tsananta.

Haka kuma, Ibrahim Abubakar Burum Burum, kansilan mazaɓar Burum Burum, ya ce bayan aukuwar bala’in sun zagaya da garin tare da ganin irin barnar da aka yi da idanunsu. Ya ce sun riga sun sanar da shugabancin ƙaramar hukumar domin ɗaukar matakin gaggawa.

Advertisement

Yanzu haka al’ummar garin Burum Burum na roƙon gwamnatin jihar da hukumomin agaji da su shigo cikin gaggawa domin rage musu raɗaɗin asarar da bala’in ya haifar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending