News
Gwamnatin Kano Ta Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Biya Diyya Kan Soke Hawan Sallah
Gwamnatin Jihar Kano ta bukaci gwamnatin tarayya da ta biya ta diyyar asarar da jihar ta yi sakamakon soke bikin Hawan Sallah na al’ada da aka dakatar a tsawon shekaru biyu a jere.
Kwamishinan Kananan Hukumomi da Masarautu na jihar, Alhaji Tajo Usman ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi, yayin da Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Alhaji Muhammadu Sanusi II, ya kai ziyarar ban girma ga Gwamna Abba Kabir Yusuf a fadar gwamnatin jihar da ke Kano.
Alhaji Tajo Usman ya bayyana cewa dakatar da wannan hawan da aka saba gudanarwa a ranakun Sallah babba da Sallah karama, ya jefa jihar cikin mummunar asara ta bangaren tattalin arziki da yawon bude ido, wanda hakan zai iya yin tasiri kai tsaye ga tsare-tsaren kasafin kudin shekara mai zuwa.
“Hawan Sallah wani muhimmin bangare ne na rayuwar al’umma da al’adun jihar Kano. Yana janyo dimbin baki daga sassa daban-daban na kasa da ma waje, kuma yana bayar da gagarumar gudunmawa wajen habaka tattalin arzikin jihar. Soke shi ya jawo wa jihar gibi da ya kamata a cike,” in ji kwamishinan.
Ya kara da cewa kasancewar gwamnatin tarayya ce ta tilasta soke bikin a shekarun baya bisa dalilai na tsaro, wajibi ne ta dauki alhakin hakan tare da bayar da diyya ga jihar Kano don rage radadin barnar da aka jawo.
“Mun yi imanin cewa jihar Kano ba za ta ci gaba da daukar nauyin wannan hasara ba, musamman duba da irin tasirin da take yi a kan tattalin arzikin cikin gida. Saboda haka, dole ne gwamnatin tarayya ta biya diyya,” in ji shi.
A baya dai, an dakatar da gudanar da Hawan Sallah a Kano sakamakon wasu matakai na tsaro da hukumomi suka dauka, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’a da masu ruwa da tsaki a harkar al’adu da zaman lafiya.
