News
Trump Ya Ce Babu Sauran Alaƙa Tsakaninsa Da Elon Musk
Shugaban Ƙasar Amurka, Donald Trump, ya ce babu sauran alaƙa tsakaninsa da attajirin nan Elon Musk, wanda a baya aka san su da kusanci sosai.
Trump ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na NBC a ranar Asabar. Ya ce yanzu haka ba su da wata alaka, kuma babu wani shirin sasanci ko komawa zama da Musk a cikin shiri ko shawara.
“Ba mu da wani abu a yanzu, kuma babu wata alaka da za ta sake kasancewa,” inji Trump.
A baya Elon Musk na daga cikin manyan mutanen da ke kusa da Trump lokacin da yake kan mulki, inda aka ba shi shugabancin wani kwamiti da Trump ya kafa domin ba da shawara kan harkokin kere-kere da ci gaban fasaha.
Sai dai daga bisani rikici ya shiga tsakaninsu bayan da suka samu sabani kan tsarin haraji da kuma kasafin kuɗin da gwamnatin Trump ta gabatar. Wannan ne ya sa Musk ya janye daga mukamin da aka ba shi, daga nan kuma aka fara samun sa-in-sa tsakaninsu.
Trump da Musk sun shafe watanni suna jifan juna da kalamai a bainar jama’a, har abin ya kai ga wannan sanarwar da Trump ya bayar cewa tuni komai ya ƙare tsakaninsu.
