News
Hatsarin Mota Yayi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 9 A Jigawa
Akalla mutane tara ne suka rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin mota da ya afku da safiyar Asabar a garin Kyaramma, karamar hukumar Ringim a jihar Jigawa.
Bayanan da Arewa Updates ta samo daga rundunar ‘yan sandan jihar sun tabbatar da cewa hatsarin ya faru ne da misalin karfe biyu na dare, inda wasu motoci kirar Golf 3 guda biyu suka yi mummunan taho-mu-gama.
An Kama Magidanci Da Ake Zargin Kashe Matarsa Mai Juna Biyu A Neja
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Lawan Shisu Adam, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa daga cikin wadanda suka mutu akwai direbobin motocin biyu, yayin da sauran su suka hada da fasinjoji. Ya kuma ce wasu fasinjoji 11 na samun kulawa a Asibitin Gwamnati da ke Ringim.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Jigawa, CP AT Abdullahi, ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, tare da jan hankalin direbobi su rika bin ka’idojin zirga-zirga domin kaucewa aukuwar irin wannan ibtila’i a nan gaba.
