News
An Kama Magidanci Da Ake Zargin Kashe Matarsa Mai Juna Biyu A Neja
Rundunar ’Yan sanda a Jihar Neja ta kama wani magidanci da ake zargi da kashe matarsa mai juna biyu a kauyen Limawa da ke cikin birnin Minna.
Lamarin ya faru ne a cikin makon nan bayan makwabta sun ji ihun da ya taso daga gidan ma’auratan, wanda hakan ya sa suka yi gaggawar shiga cikin gidan domin ceto matar mai juna biyu.
Yadda Hukumomi Ke Amfani Da Ƙarfin Iko Wajen Tauye Hakkokin Jama’a A Najeriya
Sai dai da suka shiga suka iske matar mai juna biyu a kwance rai a hannun Allah, kamar yadda wani daga cikin makwabta ya shaida wa manema labarai.
Wata majiya ta ce matar ta rasu ne sakamakon dukan da mijin nata ya saba yi mata, sai dai wannan karon abin ya yi muni, har ta rasa ranta.
A cewar mahaifin marigayiyar da ya bayyana a cikin wani shirin rediyo na Crusader’s Radio TV Show, “Yar’uwarmu ta dade tana shan wahala a hannun mijinta. Mun sha ja masa kunne, amma abin ya ci tura.”
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ya tabbatar da kama wanda ake zargin, yana mai cewa ana tsare da shi a ofishin ’yan sanda yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.
Lamarin ya haifar da ce-ce-ku-ce a cikin al’umma, inda kungiyoyin kare haƙƙin mata, sarakunan gargajiya da sauran ’yan uwa da abokan arziki suka yi Allah-wadai da abin da ya faru.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
