News
Yadda Hukumomi Ke Amfani Da Ƙarfin Iko Wajen Tauye Hakkokin Jama’a A Najeriya
A Najeriya, zalunci da tauye haƙƙin jama’a ba sabon abu ba ne, musamman idan wanda ke aikata hakan na da wani ƙarfin iko ko madafa ta gwamnati.
Yawanci idan an tauye wa mutum haƙƙinsa a Najeriya, ba a cika ganin ya tashi ya nemi ‘yancinsa ba, domin kuwa mafi yawan lokaci wanda ya zalunce shi na da ƙarfin da zai hana a tanka masa. Idan kuma hukuma ce, to kuwa lamarin yakan fi kamari.
DA DUMI-DUMI: Gobara Ta Tashi A Wani Otel Na Alhazan Najeriya A Makkah
Wani abu da ya dade yana jefa al’umma cikin kangin zalunci shi ne halin yin shiru ko nuna haƙuri a lokacin da aka cutar da mutum. Wannan hali ya jima yana zama hanya ga masu iko wajen cin zarafin jama’a babu mai ce musu uffan.
To amma alamu na nuna cewa yanzu mutane sun fara gajiya da yin shiru. Wasu na ganin cewa wannan shiru da haƙuri da aka dade ana yi ne ya sa hukumomi da wasu daidaikun mutane ke ci gaba da cutar da ‘yan kasa ba tare da fargabar sakamako ba.
A cewar wasu masu fashin baki, rashin tashi tsaye na al’umma wajen kare haƙƙinsu ne ke ba hukumomi damar ci karensu babu babbaka.
“Da zarar mutane sun daina yin shiru, kuma suka fara fitowa fili suna magana, komai na zalunci zai ragu,” in ji wani matashi da FRI HAUSA ta tattauna da shi.
Wasu na ganin cewa hanya mafi sauki ta kare haƙƙi da nuna rashin amincewa da cin zarafi ita ce zanga-zanga cikin lumana — hanyar da ke ba mutane damar bayyana damuwa ba tare da tada tarzoma ba.
Yanzu dai lokaci ya yi da jama’a za su fahimci cewa shiru ba mafita ba ne. Kare haƙƙin kai da na al’umma wajibi ne ga kowa da kowa.
-
News21 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News1 day ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
