Connect with us

News

Wata Mata Ta Shiga Hannu Bisa Zargin Hallaka Kishiyarta Da Tabarya A Bauchi

Published

on

IMG 20260928 131958 142

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta kama wata matar aure mai shekaru 33, Hauwa’u Haruna, bisa zargin kashe kishiyarta, Jamila Adamu, mai shekaru 43, a Tafawa Balewa Housing Estate da ke Bauchi.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4:05 na yammacin Lahadi, 27 ga Satumba, 2026, bayan wani rikici da ya taso tsakanin matan biyu da ke zaune a gidan mijinsu.

Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Wani Matashi Kan Zargin Hallaka Mahaifinsa Mai Shekaru 80 A Katsina

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Nafiu Habib, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin. Ya ce binciken farko ya nuna cewa wadda ake zargin ta yi amfani da Tabarya wajen bugun kishiyarta.

A cewar sanarwar, Hauwa’u ta ɗauki Tabarya ne ta bugi Jamila a goshi, lamarin da ya sa ta faɗi a sume.

Rundunar ta ce jami’an ’yan sanda na C-Division da ke Bauchi sun garzaya wurin bayan samun rahoton lamarin, inda aka kai Jamila Asibitin Kwararru na Bauchi. Sai dai likita ya tabbatar da rasuwarta.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending