News
Kotu A Amurka Ta Soke Matakin Trump Na Rufe VOA
Wani alƙali a ƙasar Amurka ya bai wa gidan rediyon Amurka (VOA) umarnin dawowa bakin aiki.
Alƙalin ya ba da umarnin dawo da ma’aikata sama da 1,000 da suke aiki a VOA wanda ya kawo ƙarshen matakin da gwamnatin Donald Trump ta ɗauka na rage yawan kuɗin da gwamnati ke kashewa wajen ɗaukar nauyin kafar yaɗa labaran.
Jami’an NDLEA Sun Kama Kunshi 510 Na Tabar Wiwi A Kano
Alƙali Royce Lamberth ce ta yanke wannan hukunci a ranar Talata inda ta ce ma’aikatan da abin ya shafa su dawo bakin aiki a ranar 23 ga watan Maris kuma lallai ne VOA ta dawo bakin aikinta.
Mai shari’ar ta ce ƙoƙarin rufe cibiyar kula da kafafen yaɗa labaran Amurka da ke kula da VOA ta saɓa ƙa’ida.
Kotun tun da fari ta bai wa gwamnatin Amurka umarnin dakatar da yunƙurin korar ma’aikata a watan Satumbar 2025.
Matakin dakatarwar na zuwa ne a watan Agusta bayan naɗa Kari Lake a matsayin shugaban hukumar kula da kafafen yaɗa labaran a farkon wa’adin mulki na biyu na shugaba Donald Trump.
A watan Maris ɗin 2025 ne shugaban ƙasar ya ba da umarnin rage ayyukan kafar yaɗa labaran.
An kafa VOA ne a shekarar 1942 bayan yaƙin duniya na II domin yaƙi da farfagandar Nazi inda kafar ke gabatar da labarai da shirye a harsuna daban-daban na duniya.
Ana kuma kallon VOA a matsayinn wani muhimmin ginshiƙi na harkokin diflomasiyyar Amurka.
Shugaba Trump ya sha sukar VOA duk da cewa akwai doka da ta tabbatar wa da VOA ‘yancin gudanar da ayyukanta ba tare da wata katsalanda ba.
Sai dai Trump ya zargi VOA da fifita labaran ƙasar Sin a lokacin da aka yi annobar Kwabid-19 da kuma zarginta da sukarsa a lokacin da yake neman takarar shugaban ƙasa a karo biyu.
