Connect with us

News

Jami’an NDLEA Sun Kama Kunshi 510 Na Tabar Wiwi A Kano

Published

on

1773911310297 750x430

‎Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa NDLEA ta sanar da kama kunshi 510 tabar wiwi tare da cafke wani mutum a Jihar Kano, gabanin bukukuwan ƙaramar Sallah.

‎A wata sanarwa da kakakin rundunar reshen Kano, Sadiq Muhammad-Maigatari, ya fitar, ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar 10 ga watan Maris bayan wani samame da jami’an suka kai bisa samun bayanan sirri.

Advertisement

An Gudanar Da Sallah Idi A Sakkwato

‎Mutumin mai suna Sani Musa, mai shekaru 34, ɗan asalin ƙaramar hukumar Bebeji, an same shi da kunshi 510 na tabar wiwi da aka matse.

Advertisement

‎A cewar NDLEA, wanda ake zargin ya amsa cewa wani dillalin miyagun ƙwayoyi da ake kira “Alaramma” ne ya ba shi kayan domin ya adana a gidansa, tare da bashi izinin sayar da su.

‎Hukumar ta ƙara da cewa an shirya sayar da wiwin ne a lokacin bakin Sallah.

Advertisement

‎NDLEA ta ce bincike na ci gaba domin cafke “Alaramma” wanda har yanzu yake tsere.

 

Advertisement

 

NAN

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending