News
Iran ta bayyana tayin Trump kan tsagaita wuta a matsayin rashin kunya
Majiyoyin Diflomasiyya daga Iran da kuma Pakistan wadda ke sahun ƙasashen da ke shiga tsakani wajen ganin an sasanta yaƙin na Amurka da Iran ta fuskar diflomasiyya sun ce matakin Iran na karɓar ƙunshin ya bada ƙwarin gwiwar iya kawo ƙarshen wannan yaƙi kodayake akwai shakku kan yiwuwar mahukuntan na Tehran su aminta da buƙatun Amurka da ke cikin wannan ƙunshi.
Gwamna Abba Ya Sauke Kwamishinan Kasuwanci Shehu Wada Sagagi Duk da yadda Trump ke ci gaba da iƙirarin samun gamsasshiyar tattaunawa da Iran tun daga kwanaki biyu da suka gabata a gefe guda Tehran na ci gaba da musantawa, sai dai manyan jami’an gwamnatin Pakistan 2 sun shaidawa AFP cewa tuni suka miƙa tayin na Trump ga Iran, sai hakan bai hana ƙasar ta gabas ta tsakiya ci gaba da kai hare-hare ba, ciki har da farmakar babban jirgin yaƙin Amurkan, a wani yanayi da kafar Aljazeera ke cewa Tehran ta yi watsi da ƙunshi na Trump.
Sai dai wasu majiyoyin diflomasiyya a yankin na gabas ta tsakiya sun tabbatar da tattaunawar ɓangarorin biyu a sirrance ta wata fuska da kowannensu ba zai ji kunyar alwashin da ya sha ko kuma rashin cikar muradansu ba, yayinda wasu daga cikin saɗarorin tayin na Trump ke nuna cewa dole Iran ta kawo ƙarshen ƙara yawan makamashin Uranium din da take tacewa tare lalata makamanta masu linzami da kuma dakatar da ƙera su, baya ga buɗe mashigin Hormuz ga kowa da kowa da kuma gamayya wajen samar da sojojin ƙasa da ƙasa wajen bayar da tsaro a mashigin, sai kuma batun janyewa Iran dukkanin takunkumai da kuma taimaka mata don sake gina kanta. Sai dai wasu majiyoyi sun ce buƙatun na Trump tun farko su ne dai buƙatun da Tehran ta ƙi amincewa da su tun a watan Yuni yayin tattaunawar ɓangarorin biyu gabanin faro wannan yaƙi.
A gefe guda Iran wadda ke neman sassaucin takunkumai na ɗaukar matakan ganin bata maimaita kuskure makamancin na yarjejeniyar 2015 da ya dakatar da ita daga bunƙasa shirinta na mallakar makamin nukiliya ba.
