Connect with us

News

Takaitaccen Jawabin Shugaba Tinubu Na Ranar Dimokuradiyya 12 ga Watan Yuni, 2025

Published

on

Shugaba Tinubu ya fara da tunawa da Ranar Dimokuraɗiyya ta gaskiya a Najeriya, wato 12 ga watan Yuni. Ya yi wa jaruman da suka sadaukar da rayukansu wajen ganin Najeriya ta samu ƴanci, musamman marigayi MKO Abiola wanda ya lashe zaɓen 1993 da aka soke.

Ya yabawa waɗanda suka yi gwagwarmaya da turjiya ga mulkin soji don ganin an dawo da mulkin farar hula. Ya ce wannan rana ta tuna da sadaukarwa da haɗin kan da suka kawo mana ƴanci.

Advertisement

Akalla Fasinjoji 200 Sun Rasu A Hatsarin Jirgin Sama A Indiya

Shugaban ya jaddada cewa dimokuraɗiyya ita ce ginshiƙin zaman lafiya da cigaban ƙasar, kuma gwamnatinsa na da ƙuduri wajen kare dokoki, ƴancin ɗan adam, da ƴancin faɗar albarkacin baki.

A ɓangaren tattalin arziƙi, ya amsa cewa ƴan Najeriya na fama da wahalhalu, musamman sakamakon cire tallafin fetur da wasu sauye-sauye da gwamnatinsa ta kawo. Sai dai ya ce waɗannan matakan suna da amfani na dogon lokaci domin dawo da daidaito a tattalin arzikin ƙasa.

Advertisement

Ya lissafa wasu matakan da gwamnatinsa ta ɗauka don rage wa mutane raɗaɗin ƙalubalen tattalin arziki, kamar: Ƙarin kuɗi na musamman ga ma’aikata, Rabon abinci, Tallafa wa manoma, da kuma Sauƙin jigilar jama’a da kaya.

Shugaba Tinubu ya buƙaci ƙarin haƙuri da haɗin kai daga al’umma, yana mai tabbatar da cewa sauye-sauyen da ake ciki suna buƙatar lokaci, amma za su haifar da alheri mai ɗorewa.

Advertisement

A ƙarshe, ya kira al’ummar Najeriya da su zauna lafiya, su ƙarfafa haɗin kai, su guji rarrabuwar kai bisa ƙabila ko addini, su kuma cigaba da kare dimokuraɗiyya domin ciyar da ƙasa gaba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending