Connect with us

News

Sojoji Sunyi Ajalin Ɗan Auta Tare Da Ƙarin Wasu Ƴan Bindigar A Zamfara 

Published

on

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 101 Sun Kama Wasu 182 A Cikin Mako Daya

Rundunar sojin Nijeriya ta ce dakarunta sun yi nasarar kashe wasu ‘yan ta’adda yayin wani samame da ta kai garin Kunchin Kalgo a ƙaramar hukumar Tsafe da ke jihar Zamfara a ranar 10 ga watan Yuni.

A sanarwar da rundunar ta wallafa a shafinta na X ranar Alhamis, ta ce rundunar FASAN YAMMA ta kashe ƙasurguman ‘yan ta’adda da suka haɗa da Auta da Abdul Jamilu da kuma Salisu.

Advertisement

Takaitaccen Jawabin Shugaba Tinubu Na Ranar Dimokuradiyya 12 ga Watan Yuni, 2025

“Waɗannan ‘yan ta’adda suna da alaƙa da ayyukan tashin hankali da ta’addanci da ake yawan samu a yankin gaba ɗaya. Wannan farmakin dai na nuni da wani gagarumin koma baya ga masu aikata laifuka, wanda ke dagula zaman lafiya da tsaro a yankin,” in ji sanarwar.

Bayanan sirri na farko-farko sun nuna cewa an kashe ƙarin wasu shugabannin ‘yan ta’adda, ciki har da wani da aka fi sani da Babaye a lokacin harin.

Advertisement

Kazalika, a wani lamarin daban, rahotanni sun ce an kashe Sale Ado Madele da aka fi sani da Sarki, babban ɗan shugaban ‘yan bindiga Ado Alieru.

A wani lamarin mai kama da haka, sojojin sun kuma kashe wasu ‘yan ta’adda goma da suka taru a kusa da wata tashar mai da ke garin Danjibga.

Advertisement

Ana kyautata zaton ‘yan ta’addan na cikin wani gungun hadin-gwiwa da Dogo Sule ya haɗa domin kai hari.

Rundunar sojojin Nijeriya ta ce tana ci gaba da jajircewa wajen kare rayuka da kuma maido da dauwamammen zaman lafiya a fadin jihar Zamfara da yankin Arewa maso Yamma.

Advertisement

“Wannan aiki yana ƙara jaddada ƙudurinmu na wargaza hanyoyin sadarwar ‘yan ta’adda tare da gurfanar da masu aikata laifuka a gaban ƙuliya.

 

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending