News
Akalla Fasinjoji 200 Sun Rasu A Hatsarin Jirgin Sama A Indiya
Akalla mutum 204 ne suka rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin jirgin sama da ya auku da safiyar Alhamis a birnin Ahmedabad, da ke arewa maso yammacin kasar Indiya.
Jirgin saman, wanda mallakin kasar Indiya ne, ya tashi daga birnin Mumbai zuwa Gatwick na Birtaniya, dauke da fasinjoji 242. Rahotanni sun ce jirgin ya fadi ne bayan mintuna kadan da tashinsa, inda ya yi karo da gidajen jama’a da ke kusa da filin jirgin saman na Ahmedabad.
Jihar Kano Ta Musanta Zargin Karɓar Sabon Bashin Dala Miliyan 6.6 Daga Ƙasashen Ƙetare
Daga cikin fasinjojin da ke cikin jirgin, Indiyawa ne 169, sai kuma ’yan Birtaniya 53, ’yan Portugal bakwai da kuma dan kasar Canada guda daya.
Hotunan da gidajen talabijin na kasar suka wallafa sun nuna yadda hayaki ke tashi daga wurin da jirgin ya fadi, tare da yadda ginin gidajen da ke kusa da wurin ya lalace. Lamarin ya jefa al’umma cikin fargaba da firgici, musamman mazauna unguwar da hatsarin ya auku.
Firaministan kasar Indiya, Narendra Modi, ya bayyana alhininsa kan aukuwar hatsarin, yana mai cewa ya kadu da faruwar wannan ibtila’i a jiharsa ta Gujarat. Haka zalika, Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda hatsarin ya rutsa da su, yana mai cewa lamarin ya girgiza shi matuka.
Ma’aikatan kashe gobara sun gaggauta zuwa wurin domin dakile wutar da ta tashi daga jirgin da kuma hayakin da ke ci gaba da fitowa daga tarkacen jirgin. Rahotanni sun bayyana cewa jirgin bai jima da tashi ba kafin hadarin ya auku.
A nasa bangaren, kamfanin Boeing ya bayyana cewa yana gudanar da bincike kan musabbabin hatsarin. A cewarsu, za su fitar da cikakken rahoto a hukumance bayan kammala tattara bayanai da tantance abubuwan da suka janyo aukuwar lamarin.
Dw
