Connect with us

News

Jami’an NDLEA Sun Kama Gungun Masu Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Kudinsu Ya Kai Naira Biliyan 5.3

Published

on

WhatsApp Image 2025 09 07 at 10.28.05 750x430

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Najeriya (NDLEA) ta ce ta tarwatsa wata ƙungiya da ke safarar hodar iblis da sauran ƙwayoyi daga Najeriya zuwa ƙasashen waje.

Hukumar ta ce ƙungiyar na da alaƙa da kasashen Ingila, Brazil, Australia da kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

Advertisement

Yadda Iyalai Da Dama Ke Shiga Rayuwar Kufai Bayan Ambaliya Ta Lalata Gidajensu

Mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi, ya ce an kama manyan shugabannin ƙungiyar uku bayan gano ƙwayoyi da aka ɓoye cikin tufafi da ake shirin aikawa Sydney, Australia, ta filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas.

Ya ce an gano hodar iblis mai nauyin kilo 17.9, wadda darajarta za ta kai sama da dala miliyan 5.3, daidai da Naira biliyan 5.3 idan ta shiga kasuwar Australia.

Advertisement

A cewar Babafemi, an kama wani da ake zargi mai suna Ogunbiyi a otel a Ikeja, inda daga baya aka gano ƙarin wiwi mai nauyin kilo 10.9, bindiga da alburusai a gidansa da ke Lekki.

Haka kuma an ce wani jigo mai suna Shola Adegoke an kama shi a wani gida da ake zargin ƙungiyar ke amfani da shi a Ikeja, inda aka gano ƙarin tabar wiwi da motocin Range Rover da Toyota Venza.

Advertisement

Hukumar ta ce bincike ya gano cewa Ogunbiyi ne ke jagorantar harkokin ƙungiyar a Najeriya, yayin da wani Adebisi Omoyele da aka fi sani da Mr. Bee ke kula da su daga Dubai.

Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa (rtd), ya yaba da ƙoƙarin jami’ansa, inda ya ce hukumar za ta ci gaba da ƙoƙarin murkushe harkar miyagun ƙwayoyi a Najeriya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending