Connect with us

News

Dokar Ta Ɓaci A Ɓangaren Ilimi Tana Buƙaci Ɗaukar Matakin Gaggawa A Kano

Published

on

Bad classroom 1280x960

Harkar ilimi a makarantun gwamnati na jihar Kano na ci gaba da fuskantar ƙalubale, abin da ke nuna cewa idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba, lamarin zai ƙara tabarbarewa.

Yawancin iyaye sun koma sanya ’ya’yansu a makarantun kudi, saboda rashin gamsuwa da halin da makarantun gwamnati ke ciki. Hakan ya jawo har ma wasu malamai da shugabannin makarantun gwamnati suka riƙa turawa ’ya’yansu makarantun masu zaman kansu.

Akwai Fargabar Rasa Rai Tare Da Jikkatar Su Yayin Rushewar Gini A Jigawa

Wata kwakkwarar magana da Dan Bello ya fito da ita a kwanakin baya, ta sake jaddada irin raguwar da tsarin ilimi a Kano ya shiga, musamman wajen lalacewar gine-gine da kayan aiki. Amma, a zahiri matsalar ta zarce haka, domin akwai batun ƙarancin ƙwararrun malamai, rashin sa ido mai kyau, da kuma halayen sakaci daga wasu malamai da ba sa zuwa makaranta yadda ya dace.

Gwamnatin baya ta sha suka kan yadda ta yi sakaci da makarantun gwamnati, har ma aka ruwaito yadda wasu filayen makarantu suka koma gidaje da shaguna. Sai dai masana na ganin lokaci ya yi da za a maida hankali wajen farfaɗo da makarantun maimakon maimaita zargi.

A wani bayani da Darakta Janar na Hukumar Ƙididdiga ta Kano ya wallafa, an bayyana cewa jihar na da makarantu firamare da sakandare kusan 9,136, inda ake hasashen kashi 70% daga cikinsu – wato kusan makarantu 6,395 – na bukatar gaggawar gyara. Idan aka dinga gyara makarantu 100 a wata, sai bayan kusan shekaru 5 da watanni 4 za a iya kammala. Wannan ya tabbatar da cewa ba zai yiwu a gyara dukkan makarantu cikin shekaru biyu kacal ba, kamar yadda ake tsammani ba

Shawarwari da ake ganin za su taimaka

Advertisement

 

Masana a ganin idan aka gina manyan makarantu guda shida (uku na firamare, uku na sakandare) cikin shekara guda, waɗanda za su ɗauki ɗalibai 1,000 kowace, tare da cikakken kayan aiki.

A ɗauki ƙwararrun malamai, tare da kafa tsarin sa ido da zai tabbatar da ingantaccen koyarwa.

A kafa tsarin biyan kuɗi daga iyaye domin tabbatar da ci gaba da kula da waɗannan makarantu, maimakon dogaro da manufar “ilimi kyauta” gaba ɗaya.

Masana na ganin cewa idan aka aiwatar da irin waɗannan matakai, zuwa shekarar 2031, jihar Kano za ta iya samar da aƙalla dalibai 5,000 masu inganci, waɗanda za su iya gogayya da takwarorinsu daga makarantun kudi a kowanne fanni.

Wannan na zuwa ne Yayin da makarantu a fadin Najeriya ke dawowa sabon zangon karatu na shekarar 2025/2026 a yau Litinin, iyaye sun koka kan yadda matsin tattalin arziki ke hana su biyan kuɗin makaranta da sauran kayayyakin karatu.

Advertisement

Rahotanni daga jihohi daban-daban sun nuna yadda tsadar rayuwa da hauhawar farashin kaya suka zame wa iyaye da ɗalibai babban cikas, inda wasu ke neman rance domin ganin ’ya’yansu sun samu ilimi.

 

 

DAILY REALITY 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending