Connect with us

News

Kwamishin ilmi mai zurfi na jihar Dr Yusuf Ibrahim Kofar ya Kaddamar Shirin duba Marasa Lafiya

Published

on

Spread the love

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA

 

Shirin tallafawa Alumma musamman musa karamin karfi da kwamishin ilmi mai zurfi na jihar Dr Yusuf Ibrahim Kofar mata ya samar domin duba lafiyar Jama’a tare da basu magani kyauta akan larurorin dake damunsu.

Advertisement

Ya samu yabo mai yawa daga bakin Alumma daban daban da suka fito daga sassa daban daban na jihar Kano domin amfanar shirin.

Manoman Da Suka Ci Bashin ‘Anchor Borrowers’ Na Cikin Tsaka Mai Wuya

Da yake karin haske ga manema labarai, jagoran kwararrun likitocin da su ka jagoranci gudanar da shirin, Yace shirin ya kunshi tsarin binkicen tantance lalurorin da suke damun mutum wato ( Medical-check-up) (da tsarin binkicen gano irin larurar da take damun lafiyar mutum) wato (Diagnosis) da kuma tsarin bada tallafin magunguna kyauta akan larurar da take damun mutum wanda aka ware Awanni masu yawa tun daga safiyar jiya Asabar zuwa daren jiya Asabar domin gudanar da aikin Wanda kwamishinan maaikatar ilmi mai zurfi ta jihar Kano Dr Yusuf Ibrahim Kofar mata ya dauki nauyi.

A jawabin da ya gabatar yayin kaddamar da shirin wanda aka gudanar a dakin taro na masallacin Sheik Ahmadu Tijjani dake Kofar mata a nan Kano, Kwamishinan ilmi mai zurfi na jihar Kano Dr Yusuf Ibrahim Kofar mata, yace an samar shirin ne domin ta ya murnar cika kwanaki dari da zababban gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf yayi a mulkin jihar Kano wanda a ka kiyasta tallafawa sama da mutane dubu uku da magunguna kyauta bayan an duba lafiyarsu tare da gano matsalolin da suke damunsu abangaran kiwan lafiya.

Advertisement

Dr. Yusuf Kofar mata har ila yau ya bukaci hadin kan Alumma domin tabbatar da nasarar shirin da sauran tsare tsaren cigaba da gwamnatin jihar Kano ke bujurowa dasu karkashin gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf.

Kazalika ya bada tabbacin cigaba da bujuro da tsare tsaren da zasu tallafi rayuwar Alumma musamman mata da matasa da sauran masu karamin karfi domin samun cigaba mai ma’ana.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *