News
Manoman Da Suka Ci Bashin ‘Anchor Borrowers’ Na Cikin Tsaka Mai Wuya
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Shirin nan na bayar da rance a harkar noma na ‘Anchor Borrowers’, wanda Babban Bankin Nijeriya ya kirkiro tare da jagoranta, domin kara bunkasa harkokin noma a Nijeriya ya fuskanci matukar koma baya, sakamakon kin dawo da kudaden da Manoman suka yi a matsayin rance.
Wannan hali na kin biyan wadannan kudade da wasu daga cikin Manoman da suka amfana da shirin suka yi, ya janyo wa sauran Manoman da ba su amfana da shirin ba tasgaro wajen samun wannan rance, lamarin da ya jefa su cikin tsaka mai wuya.
Daga cikin Naira tiriliyan 1.1, wanda Babban Bankin Nijeriya ya raba wa Manoma a matsayin rance, tun bayan kafa wannan shiri, kasa da Naira biliyan 546 kacal aka iya dawo da su, inda kimanin Naira biliyan 577 kuma, suka makale a hannun Manoman suka ki maido da su.
Wadannan makudan kudaden, sun makale ne a hannun Bankunan Hada-hadar Kudi, Gwamnatocin Jihohi, Kungiyoyin Manoma, daidaikun mutane, da kuma kamfanoni, wanda hakan ya harzuka Fadar Shugaban Kasa tare da bayyana cewa, hakan ya yi sanadiyyar gaza cimma burin da aka sanya a gaba ainahin manufar shirin.
Wata majiya mai karfi, ta sheda wa Jaridar Banguard cewa, an yi wa Shugaba Kasa Bola Ahmed Tinubu bayani a kan lamarin, inda ya yi matukar nuna bacin ransa a kan wadanda suka amfana da shirin suka kuma ki maido da wadannan kudade da aka ba su a matsayin rance. A cewar tasa, da sun maido da wadannan kudade, akwai yiwuwar wadanda ba su samu ba, su ma su samu.
Bugu da kari, daya daga cikin hukumomin tsaron ya bayyana cewa, Tinubu ya umarci daukan dukkanin matakan da suka dace na dawo da wadannan kudade daga wurin wadanda suka amfana da su, suka kuma ki maidowa daga nan zuwa ranar 18 ga watan Satumban 2023, musamman domin ainahin Manoman su amfana da su, a samu wadataccen abinci a fadin wannan kasa.
Haka zalika, an kuma shaida wa shugaban kasar cewa, Babban Bankin Nijeriya tare da ‘yan barandansa, sun karkatar da kimanin Naira miliyan 255, wadanda ya kamata a rabawa wa sauran Manoman da ba su samu ba.
Bugu da kari, an sake zargin bankuna da sauran wasu kungiyoyi a matsayin wadanda suka karkatar da naira miliyan 255, da aka karbo daga wurin wadanda suka amfana da wannan rance, amma suka ki mika wa Babban Bankin wadannan kudade.
Har ila yau, wasu daga cikin wadanda suka amfana da rancen kudaden, sun ki maido da su ne tare da yin ikirarin cewa, sun yi noman amma ba su samu wata rabar a zo a gani ba, inda suke sake bukatar a kara musu wani wa’adin, domin mayar da rance ga Babban Bankin Nijeriyar.
Tuni dai jami’ain tsaro suka fara tuhumar wasu daga cikin Manajojin Bankuna da dama a kan rikita-rikitar ta kin maido da wadannan kudade na rance, wanda akasarinsu sun amsa saba ka’idar da aka ginidaya ta maido da rancen kudaden.
Wasu daga cikin kungiyoyin da suka amfana da rancen a karkashin shirin na ‘Anchor Borrowers’, sun hada da Kungiyar Manoman Masara, Waken Suya da kuma Noman Auduga.
Kazalika, binciken Jaridar Banguard din ya sake nuna cewa, Kungiyar Manoman Masara ta karbi rancen naira biliyan 39 daga Babban Bankin Nijeriya, a karkashin wannan shiri na ‘Anchor Borrowers’.
Haka nan ita ma, Kungiyar Manoman Auduga ta karbi rancen naira biliyan 14, sannan ta maido da naira biliyan 5 daga ciki.
Har wa yau, an yi kokarin jin ta bakin mai magana da yawun Hukumomin Tsaro da ke Abuja a kan umarnin da Shugaban Kasar ya bayar na karbo wadannan kudade, amma bai ce komai ba.
Haka nan, shi ma Kakakin Hukumar Tsaro ta farin kaya (DSS), Dakta Peter Afunanya; da aka tuntube shi don jin ta bakinsa, bai ce uffan ba, sai dai ya ce, batun bayar da umarnin Shugaban Kasa; ba wani sabon abu ne ga Hukomin Tsaron Kasa.