News
Kotu ta kwace kujerar Dan majalisar tarayya na kura madobi da garum Malam ta baiwa Musa Iliyasu Kwankwaso
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Kotun sauraren kararrakin zaben yan majalisar tarayya dana jiha da ke zamanta a Kano, ta tabbatar da cewa Umar Datti Kura na jam’iyyar NNPP bai ajiye aiki ba kwanaki 30 kafin zaɓen Dan majalisar wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Kura Madobi da Garun Malam wanda aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu 2023.
Shugabar tawagar alkalan, Mai shari’a Flora Ngozi Azinge ce ta tabbatar da hakan cikin wani hukunci da ta yanke a ƙarar da Dr. Musa Iliyasu Kwankwaso da ya yiwa jam’iyyar APC takarar kujerar dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Kura Madobi da Garun Malam.
Kotun ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da ta janye Shaidar cin zabe da ta dankawa Yusuf Umar Datti tun a baya, ta kuma baiyana Musa Iliyasu Kwankwaso a matsayin wanda ya lashe zaben kuma halastaccen dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Kura Madobi da Garun Malam saboda shi ne yazo na biyu a zaben da aka gudanar ranar 25 ga watan Fabarairu 2023.
