News
Hukumar DSS Ta Kama Mataimakiyar Gwamnan Babban Bankin CBN
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) ta cafke tare ta tsare mataimakiyar gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Aisha Ahmad.
Aisha Ahmad mataimakiyar gwamnan CBN ce mai kula da daidaito a tsarin a kuɗi.
SERAP: An ba wa gwamnoni 36 wa’adin kwanaki 7 da su bayyana cikakken bayani kan kashe N2bn
Rahotanni na nuni da cewa hukumar DSS ta cafke Aisha ne bisa zargin samun hannun jari a bankunan Polaris, Titan/Union ta hanyar da ba ta dace ba.
Mataimakiyar gwamnan dai na amsa tambayoyi kan yadda bankin Titan ya samo $300m domin kammala siyan bankin Union.
An naɗa Aisha Ahmad a matsayin mataimakiyar gwamnan CBN a ranar 6 ga watan Oktoban 2017, inda ta maye gurbin Sarah Alade wacce ta yi ritaya a 2017.
Majalisar dattawa ta amince da naɗinta a ranar 22 ga watan Maris 2018.
A watan Disamban 2022, an zargi Aisha da taimakawa wajen siyar da bankin Polaris akan farashi mai rahusa domin a duba yiwuwar ba ta muƙamin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN).