News
Jami’an DSS Sun Gurfanar Da Kwamandan Ƙungiyar Ansaru A Gaban Kotu
Hukumar tsaro ta farin kaya, a Najeriya (DSS), ta gurfanar da Abdulmalik Abdulazeez Obadaki, wanda ake zargi da zama babban jagoran harin ta’addanci da aka kai wa majami’ar Deeper Life Bible da ke ƙauyen Otite, na jihar Kogi, a shekarar 2012.
A safiyar ranar 7 ga Agusta, 2012, wasu mutane uku ɗauke da bindigogin AK-47 suka buɗe wuta kan masu ibada a majami’ar.
Nan take mutane 15 suka rasa rayukansu, yayin da wasu huɗu suka mutu daga baya sakamakon raunukan da suka samu.
Tun a wancan lokacin aka alaƙanta harin da ƙungiyar Ansaru tsagin Boko Haram, wanda ya jikkata da dama bayan waɗanda suka mutu.
Bayan harin cocin Okene, rahotanni sun ce Obadaki ya jagoranci wata ƙungiyar da ta kai hare-hare kan bankuna biyar a Uromi, Jihar Edo, inda aka kashe mutane tare da kwashe kuɗaɗe masu yawa.
Daga bisani jami’an tsaro suka cafke shi suka ajiye shi a gidan yari na Kuje, amma ya tsere a lokacin da aka ɗalle gidan yarin a watan yulin 20222.
A ranar 15 ga Nuwamba, 2025, DSS ta sanar da sake cafke Obadaki bayan an kamo shi a matsayin jagoran Ansaru da ya tsere.
-
News1 day ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
