Connect with us

News

An Cafke Mutum 5 Kan Sanya Riga Mai Tambarin “Tinubu Must Go” A Borno

Published

on

Mumini AbdulKareem

Rundunar ’Yansandan Jihar Borno ta kama tare da gurfanar da wasu mutane biyar a Maiduguri bisa zargin buga da kuma sanya riga mai ɗauke da tambarin rubutun “Tinubu Must Go”.

A cewar takardar Farko ta Bayanin Laifi (FIR) da Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jiha (SCID) ya fitar, kuma jami’an kotu suka tabbatar da sahihancinta, ta bayyana cewa, waɗanda ake zargin sun haɗa da Baba Aji Gremami, mai shekaru 44; Mustapha Abba Yemen, mai shekaru 28; Abacha Mohammed Ali, mai shekaru 32; Adam Umar Gubio, mai shekaru 21; da Abdulhamid Mohammed, mai shekaru 21.

Majalisar Dokokin Rivers Ta Amince Da Kudurin Dokar Kirkiro Ƴansandan Jihohi

Takardar mai ɗauke da ranar 29 ga Satumba, 2026, ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 25 ga Satumba da misalin ƙarfe 11:00 na safe, a yankin ‘West End Roundabout’ da ke Maiduguri, babban birnin jihar.

’Yansandan sun tuhumi mutanen da laifukan hada baki wajen aikata laifi, tunzura jama’a, haddasa tashin hankali da tayar da tarzoma, da kuma daba, waɗanda masu gabatar da ƙara suka ce sun saɓa wa sashe na 60, 78, 79 da 392 na dokar hukunta laifuka ta Jihar Borno.

Lokacin da aka gurfanar da shari’ar a gaban Babbar Kotun Majistare ta 1 da ke Maiduguri, dukkan mutanen biyar sun musanta aikata laifin.

Advertisement

Daga bisani lauyoyinsu suka gabatar da buƙatar a ba su beli.

Alƙalin da ke jagorantar shari’ar ya dage sauraron karar zuwa 6 ga Oktoba, 2026, domin yanke hukunci kan buƙatar beli, yayin da aka tsara fara sauraron shari’ar kan zargin da ake yi musu a ranar 26 ga Oktoba, 2026.

 

DAILY TRUST 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending