News
“Babu Wata Kujerar Siyasa da Ta Kai Darajar Ran Dan Nijeriya” — Godswill Akpabio
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yi kira ga hukumomin tsaro da su ƙara ƙaimi wajen ceto ‘yan Nijeriya da har yanzu ake tsare da su, tare da kare al’ummomin da ke cikin barazana a sassa daban-daban na ƙasar.
Akpabio ya yi wannan kiran ne a ranar Talata a jawabinsa na maraba, yayin da sanatoci suka koma zaman majalisa bayan shafe sama da watanni biyu suna hutun majalisa.
An Cafke Mutum 5 Kan Sanya Riga Mai Tambarin “Tinubu Must Go” A Borno
Shugaban Majalisar Dattawan ya ce ƙasar ba za ta iya ɗaukar kanta a matsayin mai cikakken ’yanci ba matuƙar akwai wani ɗan Nijeriya da ke tsare a hannun masu garkuwa da mutane.
Ya bukaci hukumomin tsaro da su ƙara himma wajen ceto waɗanda aka yi garkuwa da su, tare da yin alƙawarin cewa Majalisar Dattawa za ta yi amfani da dokoki, kasafin kuɗi da kuma aikin sa ido domin gano ƙarin matakan da za a ɗauka wajen kawo ƙarshen hare-haren da ake kai wa al’ummomi.
Akpabio ya kuma yi kira da a gudanar da harkokin siyasa cikin lumana gabanin zagayen zaɓe na gaba, inda ya buƙaci ‘yan siyasa su nemi cimma burinsu ba tare da tunzura al’ummomi, ƙungiyoyin addini ko yankuna a kan juna ba.
Ya ƙara jaddada cewa ya kamata a bai wa ‘yan takara damar gabatar da shirye-shiryensu tare da amsa tambayoyi masu muhimmanci, yayin da ya kamata a bai wa ’yan ƙasa ’yancin yin zaɓinsu ba tare da tashin hankali ko tsoratarwa ba.
