Connect with us

News

Jami’an DSS Sun Kama Wasu Jami’an Tsaro Da Ake Zargin Sun Taimaka Wa Malam Nasir El-Rufai

Published

on

mallam nasir el rufai governor of kaduna state nigeria
Spread the love

Hukumar Tsaro ta DSS  ta sanar da kama wasu jami’an tsaro da ke ake zargi da amsar cin hanci wajen bai wa tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, damar kaucewa kamu a lokacin da ya koma ƙasar daga Masar a ranar 12 ga watan Faburairun da ya gabata.

DSS ta ce bayan kammala binciken da ta gudanar, ta samu wasu jami’an tsaro biyar da suka haɗar da ɗansanda da DSS da jami’in hukumar kula da shigi da fici da kuma wasu jami’an tsaron fiyalen jiragen sama da laifin amsar cin hanci, inda aka damƙasu ga hukumar ICPC, bayan da suka tabbatar da amsar na goyo.

Muna Da Mamakai Masu Linzami Sama Da 250,000 Da Za Su Ishe Mu Yaki Har Na Tsawon Shekara Biyar —Inji Rundunar Sojan Iran

Advertisement

Haka nan hukumar ta ce akwai wasu jami’an da ta kama amma ba a samesu da laifin cin hancin ba, sai dai sun bashi damar fita daga filin ba bisa ƙa’ida ba.

Idan dai ba a manta ba, a lokacin da tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya koma gida Najeriya daga Masar, jamu’an tsaro na DSS sun yi yunƙurin kama shi a tashar jiragen sama ta Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, sai dai hakarsu bata cimma ruwa ba, duk da cewa mai taimaka masa wajen hulɗa da kafafen yaɗa labarai Muyiwa Adekeye, ya ce sun kwace masa fasto ɗinsa.

Tuni dai hukumar ta shigar da shi ƙara bisa wasu tuhume-tuhumen da ta ke masa, amma kuma ta gaza gabatar da shi a gaban kotu a ranar 25 ga watan daya gabata, sabida yana hannun hukumar ICPC da ke gudanar da bincike a kansa.

Advertisement

El-Rufai dai ya musunta dukkanin zarge-zargen da ake masa, inda ya zargi gwamnati da yi masa bita da ƙulli irin na siyasa.

 

RFI

Advertisement
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *