News
Muna Da Makamai Masu Linzami Sama Da 250,000 Da Za Su Ishe Mu Yaki Har Na Tsawon Shekara Biyar —Inji Rundunar Sojan Iran
Mahukuntan sojin ƙasar Iran sun bayyana cewa ƙasar na da kimanin makamai masu linzami 250,000 a ma’ajiyarta, tare da ikon harba har zuwa makamai 800 a cikin awa guda idan buƙata ta taso.
A cewar rahoto da jaridar CMN ta wallafa ya bayyana yadda Rundunar Sojin Iran ta sha alwashin ci gaba da harba makamanta masu linzami da aka yi hasashen cewa za ta iya harba sama da 800 a rana, wannan iƙirarin na zuwa bayan da yaƙi ke ƙara ƙazanta tsakaninta da gamayyar Amurka da Isra’ila
Sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya, inda ake zargin ɓangarorin na ci gaba da nuna ƙarfin tuwo ta fuskar soji da siyasa.
Masana harkokin tsaro sun ce duk da cewa yana da wuya a tantance sahihancin alkaluman da ake ambato a irin waɗannan ikirari, babu shakka Iran na daga cikin ƙasashen da suka fi ƙarfin shirin makamai masu linzami a yankin.
Wasu Masana na gargadin cewa idan rikicin ya ƙara tsananta tsakanin Iran da Amurka ko Isra’ila, lamarin na iya shafar tsaron duniya baki ɗaya, ciki har da hauhawar farashin man fetur da kuma tangardar hulɗar diflomasiyya tsakanin manyan ƙasashe.
