Connect with us

News

Kotu Ta Yankewa Masu Garkuwa Da Mutane Hudu Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya

Published

on

edo kidnapping case judgement 1

Wata kotu ta musamman kan laifukan satar mutane da ayyukan ƙungiyoyin asiri a birnin Benin na jihar Edo, ta yankewa wasu masu garkuwa da mutane su huɗu hukuncin kisa ta hanyar rataya ko kuma ta hanyar yin allura.

Za Ka Iya Aikata Kusan Duk Wani Laifi Ka Tsallake Hukunci A Najeriya, Idan Kana Da Kyakkyawar Alaƙar Siyasa ” —  Sarki Sanusi ‎

Waɗanda aka yankewa hukuncin sun haɗar da Marvelous Isaac, Gift Raphael, Wisdom Michael, da kuma Rufus Michael an gurfanar da su ne gaban kotun bisa tuhume-tuhume 11, da suka ƙunshi ayyukan garkuwa da mutane, fashi da makami, mallakar bindigu da sauran laifuka.

 

Kotun ƙarƙashin Mai Shari’a Aigbona Terry Momodu, ta ce ɓangaren masu ƙara sun gamsar da kotun da ƙwararan hujjoji kan waɗanda ake zargi, saboda haka ta yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya ko kuma yin allura.

Rahotanni sun bayyana cewa waɗanda aka yankewa hukuncin sun yi garkuwa da wata mata ne a Kasuwar Kayan Lambu da ke kan titin zuwa Filin Jirgi a birnin na Benin, amman mijinta ya samu nasarar kuɓuta daga hannunsu.

Advertisement

CHANNELSTV ta ruwaito cewa biyo bayan faruwar lamarin Kasuwar Kayan Lambun, Gwamna Monday Okpebholo na jihar, ya kafa kotu ta musamman da za ta dinga hukunci kan ayyukan satar mutane da na ƙungiyoyin asiri.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending