News
Wata Ambaliyar Ruwa Ta Rushe Gidajen Da Dama A Abuja
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Ambaliyar ruwa ta lakume gidaje da dama a fitaccen rukunin gidaje na Trademore Estate da ke Lugbe a babban birnin tarayya Abuja.
Rahotanni na nuni da cewa Ambaliyar ta kuma lalata kadarori na miliyoyin naira sakamakon mamakon ruwan sama da aka tafka a safiyar ranar Juma’ar nan.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Kasa NEMA ta bayyanawa manema labarai cewa, ambaliyar ruwan ta tafi da direban Peugeot 406 mai lamba YLA 681 FS a kan titin Imo da ke cikin rukunin.
Haka Kuma Hukumar ta tabbatar da ceto wasu mutane 4 kuma suna cikin koshin lafiya.
Za mu farfaɗo da yardar ‘yan kasa a kan ‘yan sanda – Babban Sufeto
An ga mazauna yankin a lokacin da aka yi ruwan sama, suna kokarin ceton rayukansu da kuma ceto dukiyoyinsu bayan da gidaje suka ruahe.
Rukunin gidaje na Trademore ya shafe shekaru yana fama da munanan matsaloli na ambaliya da rasa rayuka da dukiyoyi na biliyoyin nairori.
Mazauna wannan katafaren gine-gine duk da haka sun yi gyara a lokacin daminar 2022 domin ambaliya ba ta shafe su ba duk da ruwan sama da aka samu a shekarar.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Mai gidan ya gudanar da aikin gyara wanda ya tabbatar da fadada magudanan ruwa da rushewar ginin da ke wuraren ambaliyar.
Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, masu ruwa da tsaki da suka mayar da martani kan ambaliyar da aka yi a gidajen sun hada da NEMA, Hukumar kashe gobara, FCT FEMA, Red Cross da ma’aikatar kula da muhalli ta tarayya.
