Connect with us

News

Za mu yi aiki ba dare ba rana wajen tantance ‘yan Hisba da aka kora – Babba Dan Agundi

Published

on

IMG 20250908 WA0002

Babban Darakta na Hukumar NPC na kasa, Dr. Baffa Babba Dan Agundi, ya bayyana cewa kwamitin da aka kafa domin tantance tsoffin jami’an Hisba da gwamnatin Kano ta kora, zai gudanar da aikinsa ba dare ba rana domin tabbatar da umarnin tsohon gwamnan jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

Dan Agundi ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da kwamitin mutum 44 da aka nada domin tantance jami’an Hisba 1,000 da aka sallama daga aiki a Kano.

Advertisement

“Muna da kyakkyawan Tsarin Tabbatar da Gaskiya Sama da Kowacce Jihar” – Waiya

Ya ce wajibi ne a tabbatar da duk wanda aka tabbatar shi tsohon jami’in Hisba ne, a rubuta rahoto kan halin da yake ciki domin a nemo masa mafita kamar yadda Ganduje ya umarta.

Babban Daraktan ya kuma bukaci mambobin kwamitin da su gudanar da wannan aiki cikin gaskiya da adalci, ba tare da nuna bambanci ko son zuciya ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending