Connect with us

News

“Muna da kyakkyawan Tsarin Tabbatar da Gaskiya Sama da Kowacce Jihar” – Waiya

Published

on

images 30

Gwamnatin Jihar Kano ta jaddada cewa tana da tsari mafi nagarta wajen tabbatar da gaskiya da adalci a tafiyar da mulki fiye da kowacce jiha a Najeriya.

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana haka a yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a ofishin ma’aikatar, ranar Lahadi.

Advertisement

El-Rufai Ba Shi Ne Mai Gidana Ba  —Gwamna Uba Sani

Waiya ya kuma yi kira ga ’yan jarida da su kasance masu bin ƙa’idojin aiki da adalci wajen ruwaito labarai, musamman waɗanda suka shafi shari’a da binciken hukumomin yaki da cin hanci.

Ya ce wasu kafafen yada labarai, musamman a kafofin sada zumunta, suna yada labaran da suka shafi binciken tsohon Akanta Janar na jihar, Abdulkadir Abdulsalam, ta hanyar da bai dace ba. Kwamishinan ya bayyana hakan a matsayin yunƙurin ɓata sunan gwamnatin Abba Kabir Yusuf.

Advertisement

“Aikin jarida ba lasisi ba ne na yin yaudara ko karkatar da tunanin jama’a. Abin da ake yadawa yanzu shi ne labarin da tuni yake gaban kotu, amma ana sake gabatar da shi a matsayin sabon abu,” in ji Waiya.

Kwamishinan ya jaddada cewa gwamnatin Kano ta kafa tsari na gaskiya da rikon amana wajen gudanar da mulki, ciki har da:

Advertisement

Bin dokar saye da sayarwa ta jihar (Procurement Law 2021). Kafa tsarin e-procurement domin bin diddigin kuɗaɗe ta dijital.

Duba da kuma sa ido kan ayyukan gwamnati a kowace karamar hukuma duk wata.

Advertisement

Ya ce saboda waɗannan tsare-tsare ne Kano ta zama abin koyi wajen tafiyar da gwamnati cikin gaskiya, tare da bai wa hukumar yaki da cin hanci ta jihar damar gudanar da aikinta ba tare da tsoma bakin gwamnati ba.

Waiya ya ƙara da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da tallafawa kafofin yada labarai, amma ya bukaci ’yan jarida su rike mutuncin sana’arsu, su kasance masu kishin kasa, bin ƙa’idoji da kuma gujewa yada labaran da ka iya rikita ko batar da jama’a.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending