News
Hatsarin Mota Ya Yi Sanadiyar Mutuwar Mutum 7 Tare Da Jikkata Wasu 11 A Jigawa
Wani hatsarin mota da ya faru a Jihar Jigawa ya yi sanadin mutuwar mutum bakwai, ciki har da direban motar, sannan ya jikkata wasu 11.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Shiisu Lawan Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar a Dutse.
An Kubutar Da Mata Da Kananan Yara 46 Da ’Yan Bindiga Suka Sace A Katsina
Hatsarin ya auku ne da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin Lahadi, a ranar 16 ga Nuwamba 2025, a kauyen Jigawan Kurma da ke kan titin Kiyawa zuwa Azare, a jihar Bauchi.
SP Shiisu ya ce motar, kirar Hummer, ta taso daga Kano zuwa Potiskum dauke da fasinjoji 18, inda tayoyi biyu suka fashe sakamakon gudun da ake zargin direban yana yi fiye da kima.
Mutum 11 da suka jikkata an kai su babban asibitin Dutse domin kulawa, inda aka sallami hudu daga cikinsu bayan likitoci sun duba su.
