Connect with us

News

Zafin Rana Ya Hallaka Mutum 16 A Indiya

Published

on

Zafin Rana (1)

Akalla mutum 16 ne suka rasa rayukansu sakamakon tsananin zafin rana da ya mamaye wasu sassan kudancin ƙasar Indiya tun daga farkon wannan bazara zuwa yanzu, lamarin da ya jefa miliyoyin mutane cikin mawuyacin hali.

Rahotanni sun nuna cewa wata mummunar guguwar zafi na ci gaba da addabar yankuna da dama na ƙasar, inda yanayin zafi ya haura digiri 45 a ma’aunin Celsius a wasu birane, abin da ya haddasa cikas ga harkokin yau da kullum da rayuwar jama’a.

Advertisement

Cutar Kwalara Ta Hallaka Mutane 37, Sama Da 3,000 Sun Kamu A Borno

Jihar Telangana na daga cikin wuraren da matsalar ta fi kamari, inda gwamnati ta umarci jami’anta su ƙara sanya ido tare da ɗaukar matakan kariya domin rage illar zafin ga al’umma.

Advertisement

Masana harkokin yanayi sun danganta ƙaruwar irin waɗannan guguwar zafi da sauyin yanayi na duniya, suna mai cewa matsalar na ƙara tsananta fiye da yadda aka saba gani a shekarun baya.

A babban birnin ƙasar, New Delhi, mazauna birnin na fama da matsanancin zafi da ya kai sama da digiri 40 a ma’aunin Celsius tsawon kwanaki da dama, lamarin da ya ƙara tayar da hankalin hukumomi da masana lafiya.

Advertisement

Ƙwararrun masana kiwon lafiya sun yi gargadin cewa tsananin zafi na iya haddasa bushewar jiki, kauraran jini da kuma gazawar wasu sassan jiki idan ba a ɗauki matakan kariya cikin gaggawa ba.

Saboda haka, hukumomin Telangana sun shawarci tsofaffi, ƙananan yara da mata masu juna biyu da su guji fita cikin rana, musamman a lokutan da zafin ke kai kololuwa, sai idan akwai wata lalura da ta wajabta hakan.

Advertisement

Indiya na daga cikin ƙasashen da suka fi fitar da hayaƙin da ke gurɓata muhalli a duniya, yayin da har yanzu take dogaro sosai da kwal wajen samar da makamashin lantarki, abin da masana ke ganin na taimakawa wajen ƙara ta’azzarar matsalar sauyin yanayi.

 

Advertisement

LEADERSHIP

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending