Connect with us

News

Yaro Ɗan Shekara Uku Ya Rasa Ransa Sakamakon Faɗuwa Cikin Rijiya A Kano

Published

on

images (4)

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta ce wani yaro mai shekaru uku ya rasu bayan faɗawa cikin rijiya a ƙauyen Wangara da ke Karamar Hukumar Tofa.

A cewar sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Juma’a, an samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 7:50 na safe a ranar 30 ga Janairu, bayan rahoton ɓacewar yaron tun daren Alhamis.

Advertisement

Ebonyi: Gwamna Ya Kori Kwamishina, Ya Tube Sarakunan Gargajiya Bayan Sare Kan Mutane Huɗu

Sanarwar ta bayyana cewa yaron, mai suna Abdura’uf Badamasi, ya ɓace tun daren ranar Alhamis, inda su ka ganoshi cikin wata rijiya.

Advertisement

Jami’an ceto daga hedikwatar hukumar, ƙarƙashin jagorancin darakta Alhaji Sani Anas, sun isa wurin tare da shiga rijiyar, inda suka ceto yaron cikin halin suma.

Sai dai daga bisani kuma likitoci su ka tabbatar da mutuwarsa, kuma aka miƙa gawar ga hakimin ƙauyen Wangara.

Advertisement

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta miƙa ta’aziyya ga iyalan mamacin, tare da kira ga jama’a da su kula da rufaffen rijiyoyi da sauran wuraren da ka iya janyo haɗari, musamman ga yara.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending