Connect with us

News

Ebonyi: Gwamna Ya Kori Kwamishina, Ya Tube Sarakunan Gargajiya Bayan Sare Kan Mutane Huɗu

Published

on

IMG 20230130 WA0004

Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya kori Kwamishinan Ilimi na Manyan Makarantu, Farfesa Amari Omaka, tare da tube sarakunan gargajiya da shugabannin kauyuka a yankin Amasiri na karamar hukumar Afikpo, sakamakon wani hari da ya yi sanadin sare kan mutane huɗu a jihar.

Lamarin ya faru ne a garin Okporojo, da ke yankin Oso Edda na karamar hukumar Edda, inda rahotanni ke cewa an kashe mutanen ta hanyar sare kansu tare da dauke kawunansu, lamarin da ake zargin wasu daga yankin Amasiri ne suka aikata.

Advertisement

Zazzabin Lassa Ya Yi Ajalin Mutum 17 A Jihohi 8  — Hukumar NCDC

Gwamnan ya sanar da matakan ne a ranar Asabar yayin wata ziyara ta gani-da-ido da ya kai yankin, inda ya gana da al’ummar Garin, shugabannin gargajiya, jami’an tsaro da kuma jami’an gwamnati.

Advertisement

Ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici matuƙa, yana mai cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci daukar doka a hannu ba. Ya kuma bukaci al’umma da su kwantar da hankalinsu, yana mai gargadin cewa daukar fansa ka iya kara dagula rikicin.

A cewarsa, rikicin tsakanin al’ummomin yankin ya shafe shekaru da dama duk da kokarin sasanci da yarjejeniyoyin iyaka da aka cimma a baya, wadanda ya ce ana ci gaba da karya su.

Advertisement

Saboda haka, gwamnan ya bayar da umarnin rushe dukkan tsarin shugabancin siyasa da na gargajiya a yankin Amasiri, ciki har da rushe kungiyar ci gaban gari, da kuma tubeshe dukkan shugabannin kauyuka.

Har ila yau, ya umarci korar dukkan masu rike da mukaman siyasa daga yankin Amasiri da ke cikin gwamnatinsa, yana mai cewa matakan na daga cikin kokarin dawo da doka da oda da zaman lafiya a jihar Ebonyi.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

PLATINUM POST NEWS

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending