Connect with us

News

Ana Ci Gaba Da Gwabza Ƙazamin Fada Tsakanin ISWAP da Boko Haram

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

Ana Ci gaba da gwabzawa a rikicin da ya barke tsakanin bangaren Bakoura Buduma na Boko Haram da na ISWAP an ce an kashe ‘yan ta’adda sama da 100 a tafkin Chadi da ke yankin Marte a jihar Borno.

Majiyoyi sun ce fadan wanda ya fara da misalin karfe 12 na daren ranar Asabar, yana ci gaba da gudana har zuwa lokacin da ake gabatar da wannan rahoto a wani wuri mai suna Bakuram da ke gabar tafkin Chadi.

Ƙungiyar SERAP ta buƙaci shugaba Tinubu da ya dakatar da ministocina daga karɓar fansho.

Shafin kwararen mai bibiyar harkokin tsaro na yankin Kafar labaran tsaro na yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama, ta fahimci cewa, kungiyar ISWAP na daukar fansa ne a kan sace mayakanta 60 da kwamandoji uku da kungiyar Boko Haram ta yi.

Rikicin na baya-bayan nan, a cewar majiyoyi, ya samu jagorancin wani Abou Idris, tsohon shugaban tsara yaki na Boko Haram ta Bakoura wanda ya bar su ya koma ISWAP.

Majiyar ta bayyana cewa, an samu asarar rayuka daga bangarorin biyu amma kungiyar ta ISWAP ta fi kashe ‘yan ta’addan na Boko Haram da yawa.

Advertisement

A cewar majiyar: “A yanzu haka ana ci gaba da gwabzawa kuma an kashe ‘yan ta’adda sama da 100 daga bangarorin biyu.”

Ana ci gaba da samun zama mai tsami tsakanin ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP a yankin Arewa maso Gabas.

Shafin da Zagazola Makama ya wallafa wasikar da kungiyar ISWAP ta rubutawa Boko Haram tana mai gayyatar ta da su zo dajin Sambisa a yi fadan raba gardama, inda tuni kungiyar ta Boko Haram ta amsa gayyatar.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending