Connect with us

News

Rundunar Ƴan sanda sun kama tsohon kansilan da wasu Mutum hudu bisa zargin yin fashi

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Rundunar ‘yan sandan jihar Enugu ta kama wani tsohon kansila a karamar hukumar Enugu ta Kudu bisa wasu laifuka da suka hada da shiga kungiyar asiri da kuma mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.

Advertisement

Premium Times ta ruwaito cewa Wanda ake zargin, Henry Agbo, wanda ya wakilci Ikiriki a majalisar dokokin karamar hukumar jami’an ‘yan sandan da ke yaki da ‘yan kungiyar asiri ne suka kama shi a watan Nuwamba tare da wasu mutum hudu da ke aikata irin wannan laifi.

Sauya Launin Naira da Emefiele ya yi, zamba da harƙalla ce kawai – Mai Binciken CBN

Ndukwe ya ce jami’an kungiyar masu yaki da ɓatagari a ranar 24 ga watan Nuwamba, sun kama wani da ake zargin dan kungiyar asiri ne, Chidera Ani, bisa zarginsa da hannu a asiri da sata.

Advertisement

Kakakin ‘yan sandan ya ce Ani, mai shekaru 28, ya amsa cewa shi mamba ne na kungiyar asiri na Viking Confraternity.

Ya ce an gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu tare da tsare shi a wani gidan gyaran hali a jihar.

Advertisement

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Enugu, Kanayo Uzuegbu, ya jaddada aniyar ‘yan sandan na ci gaba da dakile masu aikata laifuka a jihar,in ji Ndukwe.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending